Sojin Najeriya sun kama babban kwamandan Boko Haram

Sojin Najeriya sun kama babban kwamandan Boko Haram

- Sojin Najeriya sunyi nasaran kama daya daga cikin manyan kwamandojin Boko Haram dake cikin jerin sunayen da suke nema, a jihar Yobe                                               

- Dan kungiyar, wanda aka kamashi tare da wasu mutane biyu da ake zargi, inda ya bayyana cewar shi ya kware wajen yima yan kungiyar kiyon dabbobinsu

Sojin Najeriya sun kama babban kwamandan Boko Haram

Shidai Muhammed Bulama yana daga cikin jerin sunayen da Sojin Najeriya ke nema na yan Boko Haram, wanda shine na 105 a jerin sunayen.

Sojin Najeriya sun bayyana cewar a yakin da sukeyi na kawo karshen masu tada kayan baya a Arewa maso gabas, ta samu nasarar kama wani babban kwamandar kungiyar, cikin wa'anda ake nema ruwa a jallo.

Wannan ya biyo bayan bayanin da mai magana da yawun Sojin Najeriya Kanal Sani Usman ya fitar a Legit.ng.

Ga dai bayanin nasa Rundunar Sojin Najeriya ta samu damar cafke wani babban kwamandan kungiyar Boko Haram wanda yake a cikin jerin sunayen da muke nema, wanda shine na 105 a cikin jerin sunayen mai suna Muhammed Bulama, wanda acewar sa akwai yayansa mai suna Ardo Abba Muhammed acikin wa'anda aka kama dakuma Muhammed Kaigama, wanda aka damke su a yankin Azare, karamar hukumar Gujba a jahar Yobe, inda da taimakon yan bangan garin aka kamasu.

Sojin Najeriya sun kama babban kwamandan Boko Haram

Andai kamasu ne akan Dokuna wani kuma akan Keke suna kora Tumakai zuwa hanyar kasuwar kauyen. Alokacin da ake 'danyi musu tambaya, wanda ake zargin ya tabbatar da shine a jerin sunaye na 105 wanda Sojin suke nema, sannan kuma shi ya kwarene waje yima yan Boko Haram kiyon dabbobin su, ya kara dacewa, sunzo kyauyen nan ne domin su saida dabbobin su, saboda kudin hannun su ya kare a inda suke buya kuma daganan suyi siyayyar kayan abinci na sallah saboda sallah ta kusa.

Sojin Najeriya sun kama babban kwamandan Boko Haram

Haka kuma shugaba Muhammadu Buhari, ya bayyana rashin tsaro a kasar nan alokacin da yake jawabi a wajen yakin neman zaben Gwamnan Edo a karkashin jam'iyar APC, da za'a gudanar da zaben ranar Asabar amai zuwa.

Shugaban ya fahimci kasar tana fama da rashin tsaro, inda yayi alkawarin zai saisaita kasar a karkashin mulkinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel