Segun Abraham yace bai amince da nasaran Akeredolu ba

Segun Abraham yace bai amince da nasaran Akeredolu ba

–Dan takaran gwamnan jihar ondo karkashin jam'iyyar APC, Segun Abraham, ya ce bai amince da zaben firamaren da aka gabatar ba.

–Abraham na fadin hakane bayan ya taya Akeredolu murna

–Dan takaran gwamnan yace ya yanke shawaran ne sanadiyar tuhumce-tuhumcen da ake radawa na magudi a zaben

Segun Abraham yace bai amince da nasaran Akeredolu ba
Rotimi Akeredolu

Dr. Segun Abraham ya bayyana cewa shi fa bai amince da sakamakon zaben share fagen jam'iyyar APC da aka gudanar a ranan asabat ba, Hakazalika bai yarda da nasaran rotimi akeredolu ba a matsayin zakara a zaben.

Segun Abraham ya bayyana hakan ne bayan ya taya Akeredolu murna.

Jaridar Leadership ta bada rahoton cewa Dan takaran gwamnan yace ya yanke shawaran ne sanadiyar tuhumce-tuhumcen da ake radawa na magudi a zaben fidda gwanin da aka gabatar.

Segun Abraham yace bai amince da nasaran Akeredolu ba
Chief Segun Abraham

Abraham, wanda ya samu kuri'u 635 ya yo zargin cewa anyi rufa-rufa a cikin shirya zaben da ya ba akeredolu nasara. A wata jawabin da da diraktan yakin neman zabensa ya sa hannu, Prince Olu Adegboro, Abraham ya ce bai amince ba.

KU KARANTA:Shuwagabannin APC na kira a sake sabon zaben fidda gwani a Ondo

Akeredolu ya samu kuri'u 669, wanda ya bashi nasara a zaben. Sauran masu takara 24 sun samu kuri'u kamar haka: Olusola Oke – 576 , Ajayi Borrofice- 471 , Tayo Alasoadura- 206 , Bode Ayorinde- 67 , Jumoke- Ajasin Anifowose- 1, Tunji Ariyomo- 3, Tunji Abayomi- 5, Afemi Mayowa- 13 , Adegbomire Adebiyi- 8 , Adekunle Adekunle-  8, Ayo Akinyelure- 3 and Jamiu Afolabi, 44 , Ademola Adegoroye- 0 , Bukola Adetula – 8, Foluso Adefemi – 13 , Victor Olabimtan- 18  and Boye Oyewumi – 7.

Daliget 2774 ne aka tantance a zabem da INEC ta gabatar

Asali: Legit.ng

Online view pixel