An kama wani Fasto ya cuchi mata 499 kimanin miliyan 3

An kama wani Fasto ya cuchi mata 499 kimanin miliyan 3

An rufe wani Fasto a babban gidan yarin kirikiri sakamakon zamba cikin aminci.

Faston mai shekaru 46, wanda ake kira da suna Archie Good Marrow, an kamashi ne bayan daya cuchi wasu mata harsu 499 kuma ya gudun musu da kudin su.

An kama wani Fasto ya cuchi mata 499 kimanin miliyan 3

Faston dai yacema matan ne, ko wacce ta ajiye naira 70,000 a asusun ajiyarsa na banki, inda yayi alkawarin zai basu aron kudi kimanin naira 150,000 domin suja jali, bayan ko wacce ta sanya kudin, wanda jimillan kudin ya kama naira 3,592,800, sai kawai Good Morrow ya daina daukar wayar su, kuma ya gudu daga unguwar da yake, wanda daga baya aka kamashi a Oke Are, a jahar Ogun.

Wasu daga cikin matan wa'anda suke tare da yan sandan dake ofishin yan sanda na Pen Cinema dake Agege a jahar Legas suka kamashi daga maboyar shi sannan suka tafi dashi.

Daganan kuma aka kaishi kotu, inda yace baiyi laifi ba, wanda daga baya aka bada belinsa, sannan aka ajiye shi na wucin gadi a gidan kaso na kirikiri kafin sharuddan bada belin nashi su cika.

Me kukayi tunani?

Asali: Legit.ng

Online view pixel