An sako Ahmad Salkida

An sako Ahmad Salkida

- An sako Ahmad Salkida wanda aka kira da sunan dan jaridar yan Boko Haram

- Jami’an tsaro na sirri wato (SSS) sun sake dan jaridan nan da hukumar sojan kasarnan ta sanar da nemansa ruwa a jallo Ahmad Salkida

An sako Ahmad Salkida
Salkida

Jaridar Premium Times ta dauko rahoton an saki Salkida ne da yammacin ranar talata, 6 ga watan satumba, kwana daya bayan sun kama shi a filin tashin jirgi na Abuja. Ahmad Salkida na daya daga cikin mutane uku da hukumar soja ta sanar da nemansu ruwa a jallo kan zargin da suke musu na sanin masaniyar inda yan Bokoharam ke rike da yan matan Chibok su 200.

Shi dai Salkida yayi kaurin suna wajen dauko rahotanni kan Boko Haram, kuma an kama shi ne yayin daya sauka a filin tashin jirgi na Nnamdi Azikwe bayan ya sauka daga jirgin  Emirate mai lamba EK 785 a ranar Litinin 5 ga watan satumba.

KU KARANTA: Sojoji sun karyata labarin kama Salkida

Hukumomin kasar nan suna zargin Salkida da taimaka ma Boko Haram, sa’annan suna binciken yadda yake samun faifan bidiyon Boko Harama tun kafin sauran jama’a su gani. Amma Salkida ya musanta wadannan zarge zarge yayin da hukumar SSS ke masa tambayoyi.

Majiyarmu ta bayyana mana cewa an saki Salkida ba tare da gindaya masa sharudda ba, sa’annan sun mayar masa da dukkan kayayyakinsa da suka kwace.

A wani labarin kuma, hukumar tsaro na sirri ta fallasa cewa akwai wasu yan Boko Haram dake son shiga rundunar Soja. A wani sanarwa da ta samu sa hannun mai magana da yawun hukumar Tony Opuiyo ya bayyana cewa jami’an su sun kama wasu yan Boko Haram guda biyu a jihar Kano a lokacin da suke kokarin shigewa cikin sojoji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel