Sojoji sun kama shugaban tsageru a Niger Delta

Sojoji sun kama shugaban tsageru a Niger Delta

Rundunar sojin Najeria ta ce ta kama shugaban kungiyar tsagerun Niger Delta Avengers mai fashe-fashen bututun Mai a yankin

Sojoji sun kama shugaban tsageru a Niger Delta
Rundunar Sojin Najeria a bakin aiki a yankin Niger Delta

A wani labari da jaridar Daily Post ta buga na wata sanarwa da Kakakin rundunar sojin kasar, Kanar Sani Usman Kuka Sheka ya fitar, na cewa, dakarun briged na 13 na rundunar sojin Najeriya sun damke wani wanda ake zargin shi ne Isaac Romeo wanda ake kira G2, shugaban kungiyar tsagerun Niger Delta Avengers.

KU KARANTA KUMA: Wasu muhimman tambayoyi daya kamata tsageru su duba

A cewar sanarwar, an kama shi ne tare da wasu mutane su biyu, Lawson Samson da kuma wani tsoho Iyang Ekpo a garin Kalaba ta jihar Kross Ribas, a yayin da suke tafiya a mota; an kuma samu nasarar kama su ne tare da hadin gwiwar jami’an Sojojin Ruwa da na Sama da kuma na bangaren Hukumar Leken asiri.

Sanarwar ta kuma cigaba da cewa, “an samu nasarar kama su ne bayan da aka rika bibiyarsu a wani shiri da suke yi na sake kai hari don durkusar da wasu muhimman kayayakin hukuma na ci gaban kasa. Kuma ana nan ana ci gaba da yi musu tambayoyi".  

KU KARANTA KUMA: Kungiyar matasa sun yiwa Tsageru bara'a

A wani labarin kuma, a cewar sanarwar, Rundunar sojin ta yi nasarar kama wani tsagera mai suna Gabriel Ogbudje wanda ake zargi da fasa babban bututun Mai na kamfani NPDC mai fitar da Mai daga teku, wanda kuma ya ratsa ta babban yankin Ogo-Oteri.

Asali: Legit.ng

Online view pixel