Mutane sun yi ca akan Masari saboda kyautan makara da yayi

Mutane sun yi ca akan Masari saboda kyautan makara da yayi

Yayinda yan Najeriya ke tofa albarkacin bakinsu akan mawuyacin halin da ake ciki, gwamnan jihar katsina, Aminu Bello Masari, ya saya makara 3,000 ya rabawa Masallatai.

Mutane sun yi ca akan Masari saboda kyautan makara da yayi

Game da wani marubucin yanar gizo, Jamil Maba, ya ce an saya ko wani guda daya N40,000.

Mabai ya gauraya shafinsa ta twita ya bayyana abinda ya faru kuma ya kushe yin hakan, a maimakon biyan ma'aikata da kuma shawo kan matsalolin da ke kasa, gwamnan na ta sayan makara da kudin jama'a.

A jihohi da dama a Najeriya, ma'aikata na bin kudin albashi banda masu katban fanshon da aka manta da su.

KU KARANTA:Buhari ya fara garambawul a Najeriya – Ngige

Kasar nanan na fuskantan matsalolin durkushewan tattalin arziki wanda yayi sanadiyar hauhawan kayan masarufi.

Ga maganganun shi

Shin me muka yi da za'a yi mana wannan wulakanci,a maimakon biyan albashin mutane ana sayan makara 3000 a farashin 40,000 ga kowanne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel