PDP ta kai karan Obaseki Kotu

PDP ta kai karan Obaseki Kotu

- Jam'iyyar PDP ta kai dan takaran gwamnan jihar Edo karkashin jam'iyyar APC, Godwin Obaseki kotu

- PDP ta tuhumci Obaseki da laifin karyayyaki a takardun karatunsa

- APC tace zatayi farin cikin haduwa da PDP a kotu

Yayinda ake samun labarin goyon bayan Shugaba Muhammadu Buhari ga dan takaran gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ke cigaba da yaduwa, jam'iyyar PDP ta fara zagon kasa.

PDP ta kai karan Obaseki Kotu
pdp c

Jam'iyyar PDP ta nemi kotu ta dakatar da Obaseki daga takara a zaben da za'a gudanar a karshen mako ta dalilin karyayyakinda yayi akan takardun bokonsa da ya mika ma Hukumar gudanar da zabe na kasa mai zaman kanta INEC.

Jam'iyyar PDP ta nemi kotun ta fadi cewan maganan da obaseki yayi na cewan ya karasa karatunsa a Jami'ar Ibadan da kwalin digri a shekarar 1976,karkashin NEC form CF001 at Part B, paragraph C dated 11 July 2016, karya ne. Kana jam'iyyar adawan ta nemi kotu da ta dakatad da obaseki daga takara a zaben da za'a gudanar a ranan asabar.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya sauka jihar Edo

Game da cewar Jaridar vanguard, shugaban jam'iyyar PDP, shiyar jihar Edo, Cif Dan Orbih ya fadi a wata hira da yan Jarida cewan ya zaman wajibi PDP ta kai karan saboda takardun karatun da obaseki ya rantse yanada shi karya ne. Cif orbih ya kara da cewa obaseki yaki karyata hakan bayyana ainihin takardun bayan yace an gano su a kasat amurka. Yana kira ga masu zabe da cewan kada suyi asaran kuri'un su saboda APC ba tada dan takara.

Orbih ya kara da cewan banda yaudarar INEC da yayi, obaseki yaki bayyana cewa ko shi dan wani kungiyaan asiri ne ya cacanta a dakatad dashi daga takaran gwamnan jihar Edo. A karshe, shugaban PDP yace obaseki bai cika sharudan kundin tsarin mulki Section 182 (I) h na takarar gwamnan jiha ba. Saboda haka kotu ta dakatad dashi.

Shugaban yakin neman zaben Obaseki, Mr Osarodion Ogie ya mayar da martani ta cewa: “Ba zamu basu amsa ba, PDP ta kusa karewa a Edo kuma akan wannan zance ,zamu hadu a kotu.

A bangare guda, jiya ne shugaba Buhari ya je tarin yakin neman zaben Godwin Obaseki a filin kwallon Samuel Ogbemudia stadium, Benin, Edo. Inda ya taya gwamnan murna tun kafin zabe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel