Jami’o’in da suka fitar da sunayen sababbin dalibai

Jami’o’in da suka fitar da sunayen sababbin dalibai

Jerin Jami’o’in da suka fitar da sunayen sababbin dalibai.

Jami’o’in da suka fitar da sunayen sababbin dalibai

 

 

 

 

Samun shiga Jami’a bana, ba abu bane mai sauki, ko kusa. Tun da Gwamnati ta soke Jarrabawar ‘Post UTME’, don hala Jami’o’i suka kirkiri hanyoyin dabam na daukar dalibai.

Mun kawo maku wasu daga cikin Jami’o’in Kasar nan da tuni suka fitar da jeringiyar sabbabin dalibai da suka dauka. Ga su kamar haka:

Jami’ar Babcock

Kungiyar Cocin ‘Seventh-day Adventist’ ke da Jami’ar ta Babcock wanda ke tsakanin Garin Ibadan da Legas. Tana da dalibai da dama, Jami’ar ta fitar da jerin sababbin dalibai da ta dauka a yanar gizo.

Jami’ar Ajayi Crowther

Jami’ar Ajayi Crowther da ke Garin Oyo ta fitar da jeringiyar sababbin dalibai a shafin makarantar na yanar-gizo. Haka dai wannan Jami’ar tana karkashin wani Cocin Angelika ne.

Jami’ar Bowen

Idan har ka cike Jami’ar Bowen da ke Jihar Oyo, sai ka garzaya shafin makarantar na yanar-gizo domin ganin ko kana da rabo.

Jami’ar Afe Babalola, Ado

Jami’ar Afe Babalola (ABUAD) da ke Garin Ado-Ekiti na Jihar Ekiti ta fitar da jerin sabbabin daliban ta da za su karanta ilmin kimiyya, fasaha, likitanci dsr. Jami’ar Afe Babalola dai ta wani Attajiri ne mai suna Emmanuel Afe Babalola.

KU KARANTA: Hukumar INEC ta shirya gudanar da zaben Edo

Jami’ar Chrisland

Jami’ar Chrisland da ke Garin Abeokuta a Jihar Ogun ta fitar da sunayen sababbin dalibai a yanzu haka.

Jami’ar Igbinedion

Jami’ar Igbinedion da ke Garin Okada, a Jihar Edo ta fitar da sunayen sabbabin dalibai da za ta dauka wannan shekarar.

Jami’ar Veritas ta Abuja

Wannan it ace Jami’ar Katolika ta farko a Kasar nan, yanzu haka ta fitar da jeringiyar sababbin daliban ta. Tana Garin Abuja.

Jami’ar Covenant

Jami’ar Covenant da ke Garin Ota na Jihar Ogun ta fitar da sunayen sabbabin dalibai na wannan shekarar.

Akwai har wa yau dai su Jami’ar American University da ke Yola, Reedemers da sauransu.

Sai dai ban da wadannan da yawanci ban a Gwamnati bane, akwai Jami’o’in Gwamnatin da su ka fitar da Jeringiyar sunayen sababbin daliban su, irin su: Jami’ar Bayero ta Kano, Jami’ar Jihar Kwara, Jami’ar Jihar Nasarawa, Garin Keffi, Jami’ar Fatakwal, Jami’ar DELSU dsr.

Asali: Legit.ng

Online view pixel