Za mu shawo kan matsalar tattalin arziki-Inji Shugba Buhari

Za mu shawo kan matsalar tattalin arziki-Inji Shugba Buhari

– Shugaba Buhari na Najeriya yace Najeriya tana cikin wani mawuyacin hali

– Shugaba Buhari yace abubuwa za su yi kyau nan gaba

– Shugaban Kasa ya kuma ya yaba da ayyukan Gwamna Oshiomhole a Jihar Edo

Za mu shawo kan matsalar tattalin arziki-Inji Shugba Buhari

 

 

 

Shugaba Buhari yayi magana game da halin tattalin arzikin Kasar nan, ya kuma sa ran cewa abubuwa za su yi kyau nan gaba. Shugaba Buhari yayi wannan maganar ne yayin da ya je taron kamfen din takarar Gwaman Jihar Edo, inda ya goyi bayan Godwin Obasekin na APC. Buhari ya tabbatar da cewa kwanan nan abubuwa za su yi sauki a Najeriya.

KU KARANTA: Shugaba Buhari zai je Edo yawon kamfen din APC

Najeriya ta shiga cikin wani hali na rugujewar tattalin arziki, sai dai Shugaba Buhari yace zai cigaba da ganin cewa an fita daga wannan matsala. Jaridar Leadership ta rahoto Shugaban Kasar ya yaba da ayyukan da Gwamna Adams Oshiomhole yayi a Jihar, ya kuma taya dan takarar APC Obaseki murna. Shugaba Buhari ya tunatar da mutanen abin da ya fada shekaru talatin da suka wuce, yace: ‘Najeriya muna da arziki; muna kuma da matasa da dama, ba mu da inda ya wuce Najeriya, duk inda mu ka je, a dawo dai Najeriya ce Kasar mu. Ya zama dole mu tsaya mu gyara Kasar mu!’

Shugaba Buhari ya taya dan takarar APC, Godwin Obaseki murna, ya kuma mara masa baya, Shugaba Buhari yace Obaseki kwararren mutum ne don haka mutanen Jihar su zabe sa, idan har suna son cigaba da ganin aiki a fadin Jihar.

Shugaba Buhari yace an ci karfin matsalar tsaro, haka kuma za ayi kokari wajen gyara tattalin Kasar nan. Najeriya za ta dawo da kimar ta inji Buhari. Muhammadu Buhari yace za muyi alfahari da yawan mu da girman mu, Najeriya ba za ta zama girman kawai ba!

Asali: Legit.ng

Online view pixel