Ana kiran Nnamdi Kanu Shugaban Biafra a gidan Yari

Ana kiran Nnamdi Kanu Shugaban Biafra a gidan Yari

– Nnamdi Kanu ya zama Sarki a Gidan kurkukun Kuje

– Charles Okah ya bayyana cewa ana kiran Kanu da Shugaban Kasar Biafra a gidan Yarin

– Charles Okah yace Dabi’ar Kanu ta sa da dama suka koma Kungiyar TRIPOB

Ana kiran Nnamdi Kanu Shugaban Biafra a gidan Yari

 

 

 

 

Charles Okah yace Nnamdi Kanu ba shi da halin kaskantar da kan da zai sa wasu su goyi bayan tafiyar sa, a cewar Okah, Shugaban Kungiyar ta ‘Indigenous People of Biafra’ (IPOB) Nnamdi Kanu, ba shi da tawalin da Shugaba ke bukata. Charles Okah na tare da Nnamdi Kanu inda suke daure a Gidan Yarin Kuje, Okah ya bayyana cewa sauran ‘yan kason suna kiran sa (Shi Kanu) da ‘Ranka ya dade, Shugaban Biafra.’

Kwanan nan wata Kungiyar da ta ware daga Kungiyar IPOb ta nada shi Charles Okah a matsayin Shugaban ta. Okah, Shugaban wata Kungiyar da ta bangare, yace Kanu yana da girman kan tsiya, don haka ba zai iya jagorantar Mutanen Biafra ba.

KU KARANTA: Canji, Canji, Kafin Canji ya zo, wasu sun mutu.

Okah dai ya karbi kiran da Kungiyar ‘Rebranded Indigenous People of Biafra’ (TRIPOB) da kuma ‘the Renegade Indigenous People of Biafra’ (RENIPOB) suka yi masa, Okah yace, girman kai, rawanin tsiya ne. Okah yace yanzu haka, Kanu yana kiran kan sa Shugaban Kasar Biafra, kuma yana yawo da mukarrabai ana kiran sa ‘Excellency’ Watau ‘Ranka ya dade!’ Okah yace wannan dabi’ar ta sa Jama’a suka bangare zuwa sabuwar Kungiyar TRIPOB. A matsayin san a Shugaban sabuwar Kungiyar ta TRIPOB, Okah yace babu batun yada tutar Biafra, babu gudu, babu ja-da-baya. Okah yace ba za su karaya ba, kuma ba su tsoron kowa.

Okah ya bayyana cewa Lauyan sa, Mr Timipa Jenkins Okponipere, Esq ne dai ya sanar da shi cewa Kungoyoyin ‘The Rebranded Indigenous People of Biafra’ (TRIPOB) da kuma ‘Renegade Indigenous People of Biafra’ (RENIPOB) sun masa mubayi’a a matsayin Shugaba yana Gidan Yarin Kuje.

Asali: Legit.ng

Online view pixel