Dangote ya karyata jita-jitan cewar ya sanya guba a shinkafa

Dangote ya karyata jita-jitan cewar ya sanya guba a shinkafa

ByByKamfanin Dangote yayi karin dangane da jita-jitan dake yawo akan shinkafar da kamfanin ta samar, Acewar bayanan da suka fitar, shinkafar Dangoten an dai shukarane a cikin gida, kuma tanada inganci mai kyau.

Dangote ya karyata jita-jitan cewar ya sanya guba a shinkafa

Acewar karerayin dake yawo yana nuna cewar kamfanin Dangoten tare da Gwamnatin tarayya sun hada hannu domin su shugo da shinkafa mai suna GMO, wanda akasa guba daga kasashen waje a inda kamfanin tace wannan karya ne tsagwaronta; Dangote baya daga cikin wa'anda ke noma ko kuma saida shinkafar GMO. Kuma ayi bincike a Najeriya ko kuma a wani waje daban.

Abunda ya kamata mutane su Gane anan shine noma akasa da kamfanin Dangoten takeyi na noma shinkafa tun shekarar 2014 bayan da kamfanin ta daina shugo da shinkafan ta fara nomawa a cikin gida.

Kalli zahiri da kanka!                                       - shekarar 2014: Dangote ya sanya hannun yarjejeniya tare da Gwamnatin tarayya na kimanin kudi dalar Amurka biliyan daya, domin noman shinkafa a jahohin Kebbi, Niger, Kwara, Jigawa.

A shekarar 2016: Ya fara bunkasa harkar nomar shinkafa na biliyoyin naira inda akayi da filin nomar shinkafa mai girman hecta 8000 a Hadeja jahar Jigawa.              - A shekarar 2016: Ya samar ma da mutane aiki kimanin mutum dubu 10,000 ( kai tsaye da kuma wa'anda aka labasu) domin bunkasa noman shinkafa.

- Haka kuma ya samar da iri mai inganci wanda ake cema FARO 44, wanda ma'aikatar noma ta tabbatar da ingancin sa, ya kuma rabama manoma domin bunkasa harkar nomar shinkafa.

Dalilin duk wa'dannan abubuwan, domin kawo karshen amfani da shinkafar waje, don inganta noman shinkafar Dangote dan ganin anyi amfani da ita ako ina a fadin kasar nan.

Haka kuma, tayayya za'ayi ace kamfanin Dangote wanda yayi suna a ko'ina zai iya yin irin wannan abun bayan ma akwai hukumomin dake kula da ingancin abinci da aka shugo dashi ko kuma aka noma a kasa, irin su NAFDAC, SON, CPC, sannan ace kamfanin Dangote ta shugo da shinkafa mai guba.

Ku taimaka ku yada saboda gaskiya tayi aikin ta!!!

Asali: Legit.ng

Online view pixel