Buhari baida laifin kan koma bayan tattalin arziki- Lalong

Buhari baida laifin kan koma bayan tattalin arziki- Lalong

- Gwamnan jihar Filato Simon Lalong ya bayyana tabbacin cewa, gwamnatin Buhari zata gyara tattalin arziki

-Yace gwamnatin jihar zata raya aikin noma da kuma sassan ma’adinai a jihar Filato

Buhari baida laifin kan koma bayan tattalin arziki- Lalong
Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong

Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong ya barrantar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari daga ko wani laifi game da halin koma bayan tattalin arziki.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa Lalong ya kuma bayyana tabbacin cewa gwamnatin Buhari zata gyara matsalar tattalin arziki.

Lalong, da yake Magana a ranar Litinin, 5 ga watan Satumba, a gurin taron da akayi a gidan gwamnati, garin Jos, kan kaddamar da sabon mataimakinsa, yace za’a rayar da aikin noma a jihar Filato.

KU KARANTA KUMA: Dubi asibitin da ya fi ko wanne lalacewa a Najeriya (Hotuna)

A gurin taron, Lalong ya rantsar da masu bashi shawara na mussaman guda hudu.

A halin yanzu, jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari kada ya tayar da hankalisa kan makircin jam’iyyar adawa wato Peoples Democratic Party (PDP).

Jam’iyyar ta nemi da shugaban kasa ya ci gaba da mayar da hankalisa a kokarinsa na ganin ya inganta tattalin arzikin kasa, jaridar Vanguard ta ruwaito.

A wata sanarwa da a kari a Abuja a ranar Litinin, 5 ga watan Satumba, daga hannun sakataren kasa baki daya, Mai Mala Buni, jam’iyyar APC tace PDP na kokarin ganin ta shafa wa gwamnatin Buhari bakin fenti.

Asali: Legit.ng

Online view pixel