Shuwagabannin APC na kira a sake sabon zaben fidda gwani

Shuwagabannin APC na kira a sake sabon zaben fidda gwani

-Shuwagabannin APC na kira a sake zaben kan zargin magudin zabe

-Shuwagabannin jam'iyyar sunce an fitarda bakin sunayen wakilai daren ranar zaben, bayan an kwanta

-Sunce wadannan sunayen akayi amfani dasu wajen zaben

Shuwagabannin APC na kira a sake sabon zaben fidda gwani
Segun Abraham

Zaben fidda gwani na jam'iyyar All Progressives Congress a jihar Ondo ya jawo kace-nace domin wasu shuwagabannin jam'iyyar na kira a sake zaben.

Shuwagabannin sun bukaci haka a wata takardar koke da suka aikama shugaban kwamitin duba Koke-koken zaben, cewar The Punch. Wadanda suka sama takardar koken hannu sun hada da wani tsohon shugaban mazabar tsakkiya ta jam'iyyar Adegboyega Adedipe da kuma shuwagabannin kananan hukumomin Ondo ta gabas da ta yamma Akintunde Samuel da Adeola Ademulegun. Sunyi zargi yin magudi a zaben da kira da a sake sabon zabe.

Takardar koken na cewa wanda an soke koko canza kashi 47 na sunayen wakilan Ondo ta gabas da sunayen da ba'a sansu a matsayin 'yan jam'iyya ba. Wadansu daga cikin sunayen da akasa basu ma san anyi haka ba, dalilin rashin zuwansu wajen zaben.

Shuwagabannin APC na kira a sake sabon zaben fidda gwani
Rotimi Akeredolu, APC

"An saka sunaye 64 a cikin sunayen wakillan wadanda ba'a sansu ba cikin jam'iyyar. Misali wani wanda bai taba takarar zabe ba, da wadanda ba'a sansu ba, kwaram sai suka zama shuwagabannin mazabun shidda, hudu, biyu da bakwai na Karamar hukumar Ondo ta gabas"

KU KARANTA:Olusegun Abraham ya taya Akeredolu murna

Wani tsohon shugaban kungiyar lawyoyi ta kasa Chief Rotimi Akeredolu (SAN), yaci zaben inda zai tsaya takarar zaben gwamna da za'a yi ranar 26 ga Nuwamba.

Asali: Legit.ng

Tags:
APC
Online view pixel