Yan bindiga sun sace malamin coci a Warri

Yan bindiga sun sace malamin coci a Warri

-Sace-sacen mutane a kasar Najeriya na ci gaba da yawa

-Wani malamin cocin Catholic shine sabon mutumin da aka sace a yanzu

-Al’amarin ya faru ne a garin Warri, jihar Delta

Wasu da ake zargin Yan bindiga ne sun sace wani malamin cocin catholic, Rev. Fr. Paul Irikefe, a garin Warri, jihar Delta, jaridar Punch ta ruwaito.

Yan bindiga sun sace malamin coci a Warri
Inpekto janar na yan sanda, Ibrahim Idris Kpotu

An sace Fr. Irikefe, wanda aka ce Lactara ne a mayan cocinan Saints Peter and Paul Catholic a Bodija, jihar Oyo, a jiya 5 ga watan Satumba.

Rahoto ya nuna cewa malamin cocin ya isa jihar Delta a jiya domin halartan jana’izar abokinsa kuma abokin aikinsa Rev. Fr. Ameafule Chike.

KU KARANTA KUMA: MD ya mutu sanadiyar bin motar bas da ta gogi motarsa

Zakuji cikakken bayani daga baya…..

Cikin rahotanni makamantan wannan, a makon da ya gabata, hukumar yan sandan jihar Lagas sun kama masu satan mutane da ake nema da kuma shugaban kungiyar yan bindiga a jihar.

Wanda aka kama mai suna Peretun Governor. Hukumar yan sanda dama na neman sa ruwa a jallo. Amma bayan an kama shi, an rahoto cewa Fasto din wanda ya bayyana sunan sa a matsayin gwamna Peretun, ya karyata zargin.

yace yana shirin shiga mota a tashar Iba, domin tafiya jihar Ondo lokacin da yan sanda suka kama shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel