Wasanni: An kawo labarin gasar kwallon kafa

Wasanni: An kawo labarin gasar kwallon kafa

A ranar Lahadi aka kammala wasannin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka da Gabon za ta karbi bakunci a 2017, kuma tuni aka samu kasashe 16 da za su kara a gasar.

Kasashen sun hada da Algeria da Burkina Faso da Kamaru da Cote d'Ivoire da Jamhuriyar Congo da Masar da Ghana da Guinea Bissau.

Sauran kasashen sun hada da Mali da Morocco da Senegal da Togo da Tunisia da Uganda da Zimbabwe da mai masaukin baki Gabon.

Uganda wadda ta yi ta biyu a rukuni na hudu da maki 13 da Togo wadda ta hada maki 11 a rukuni na daya a mataki na biyu, sune suka cike gurbi.

Guinea-Bissau ce kasar da za ta fara halartar gasar kofin Afirka a karon farko, yayin da Senegal ce wadda ta lashe dukkan wasannin neman shiga kofin na Afirka.

Za a fara yin gasar kofin Afirka a ranar 14 ga watan Janairu zuwa 5 ga watan Fabrairun 2017.

Asali: Legit.ng

Online view pixel