DSS ta kama yan Boko Haram

DSS ta kama yan Boko Haram

-DSS ta kama 'yan Boko Haram biyu na kokarin kutsawa cikin soja

-Jami'an tsaro sunce 'yan ta'addar masu hada bama-bamai ne domin cutar da sojoji

-Ta bukaci 'yan Najeriya masu bayanai sahihai su bayar domin tsaron kasa

Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) tayi yekuwar shirin Boko Haram na shiga soja. Wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Tony Opuiyo ya bayar na cewa jami'an tsaro sun cafke 'yan Boko Haram biyu a jihar Kano na kokarin shiga soja. Yace:

"Yayin da 'yan Boko Haram ke sake matattararsu a jihar Kano, hukumar tare da hadin kan hukumar sojoji sunyi wani aiki wanda ya jaza kama wasu manyan 'yan Boko Haram biyu masu sunaye Ibrahim Ustaz Abubakar da Idris Audu (aka fi Sani da AYA). Audu dai ana shirya shi domin samun kafar shiga jami'an tsaron kasar. Audu ya shirya dabarun shiga soja a daukar sojoji na gaba kafin a kama shi".

DSS ta kama yan Boko Haram
Soldiers

Ya cigaba da cewa an fatattaki gungunan masu satar mutane domin amsar fansa a garuruwa da yawa cikin kasar, yana kuma rokon jama'a masu sahihhan jawabai su bada su domin tsaron kasa

Sanarwar ta cigaba da cewa, ranar 22 ga Agusta mun kama wani Samuel ASUQUO, wanda jigo ne wajen satar mutane domin amsar fansa a kauyen Nasarawa Bakoko a jihar Cross Rivers. ASUQUO nada hannu cikin satar 'yan Australia ukku ma'aikatan kampanin siminti na Lafarge wanda gungunsa suka amshi kudin fansa mai yawan naira miliyan dari da hamsin (N150m)

Haka kuma ranar 30 ga Agusta mun kama wani mugun  gungun masu satar mutane su ukku, Bamaiyi MUSTAPHA (aka fi sani da Dan Borno), Aminu ISA and Hassan SHEHU, tsakanin Abuja-Kaduna a garin Lafia a jihar Nasarawa. Gungun sun sace wasu mata 'yan kabilar Igbo wanda suka amshi kudin fansa na naira miliyan sha ukku (N13m). Hukumar ta kama su yayin da suke shirin wata gagarumar sata a Abuja.

KU KARANTA : Wasu Sojoji na sayar da makamai ga ‘yan Boko Haram

A wani samame da aka kai garin Tamburawa, tsakanin Kano-Zaria an kama wasu muggan masu satar mutane da kuma fashi da makami masu sunaye Alhassan MUSA da Ado Yusuf, wadanda ke ayyukansu a dajin Falgore na karamar hukumar Doguwa ta jihar kano.

A wani labarin kuma, hukumar ta Kama wani mai suna Abbas MOHAMMED a Asokoro, Abuja. Shi dai an same shi da laifin aikama jakadan kasar Ukrain a Najeriya da sakunnan barazana. Binciken farko ya nuna cewa Mohammed tsohon direba ne a ofishin jakadan wanda ya fara aika sakunnan barazanar bayan an sallameshi aiki domin rashin da'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel