Abokin Jonathan ya koma APC

Abokin Jonathan ya koma APC

Abokin siyasan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan Farfesa Richard King ya yarda kwallon mangwaro ya huta da kuda, inda ya fita daga jam’iyyar PDP ya koma APC.

A cewar King, ya zama dole ya fita daga jam’iyar dake fama da rikice rikice zuwa jam’iy mai alkibla, inji jaridar The Nation.

Abokin Jonathan ya koma APC
Farfesa King

A lokacin da yake karin bayani kan fitar sa daga jam’iyar PDP a birnin Uyo na jihar Akwa Ibom, King yace PDP ta dargaje sakamakon rashin bin doka da ka’ida. yace wanda gaskiya PDP ba zata iya cika mana burikan mu ba. Abin takaici ne ganin yadda jam’iyar ba zata iya samar da jama’an jihar Akwa Ibom ababen more rayuwa ba da dimokradiya na gari.

Da wannan dalilin ne, da kuma kasancewa na dawo daga rakiyar gwamnatin jihar nan da kuma rashin iya mulki na gari daga jam’iyar PDP, hakan yasa a yau ni da magoya baya na mun koma jam’iyar APC. Ina rokon ku da kuma ku dawo jam’iyar APC saboda irin hangen nesan ta da sanin ya kamata don cigaban kasar nan.

Abokin Jonathan ya koma APC

Shi dai farfesa King dan karamar hukumar Ikot Ebok na daya daga cikin mutane 22 da suka nuna sha’awar tsayawa takarar gwamna a zaben shekara 2015 a jam’iyyar PDP. Sai dai su duka sunki shiga zaben fidda gwanin da ya fitar da gwamna Udom Emmanuel a matsayin dan takarar jam’iyar sakamakon zargin da suka yin a cewa wani ne kawai keson cigaba da mulkan jihar.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel