Sultan ya sanar da ranar Sallah

Sultan ya sanar da ranar Sallah

A ranar juma’a 2 ga watan satumba ne mai alfarma sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar III ya bayyana ranar litinin 12 ga watan satumba a matsayin ranar idin babbar Sallah.

Sultan ya sanar da ranar Sallah

Wata sanarwa da ta samu sa hannun shugaban kwamitin dake baiwa sarkin musulmi shawara kan harkokin addini Alhaji Sambo Junaidu, tare da mambobin kwamitin ganin wata ta tabbatar da ranar 3 ga watan satumba a matsayin 1 da watan Zulhijja shekara ta 1437 bayan hijiran Annabi Muhammadu SAW.

Biyo bayan amicewa da rahotanni kwamitoci da dama, mai alfarma Sarkin Musulmi ya sanar da da ranar litinin 12 ga watan satumba a matsayin 10 ga watan Zulhijja, wanda hakan ke nuna ranar a matsayin ranar Idin babbar Sallah.

Sa’annan sarkin ya taya al’ummar musulmai murna, kuma yayi musu fatan shiriyar Ubangiji Allah tare da kariyarsa, da kuma albarkar sa, daga bisani kuma ya bukaci musulmai da su cigaba da yi wa kasa addu’ar samun dawwamammen zaman lafiya da sabon arziki.

A wani labarin kuma hukumar yaki da fatauci da shan miyagun kwayoyi NDLEA ta cafke wata mata yar sheara 55 dauke da miyagun kwayoyi. An kama matar mai suna Basira Binuyo ne a tashar tashin jirage na Murtala Muhammed dake Abuja yayin binciken da ake ma matafiya zuwa birnin Madina.

Hukumar ta bayyana cewa Binuyo ta yi kashin sama da kunshi 76 na hodar Iblis, sannan za’a cigaba das a ido don ganin ta fitar da duk abin da hadiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel