Inyamurai da Hausawa sun amince da yin aiki tare

Inyamurai da Hausawa sun amince da yin aiki tare

- Inyamurai da Hausawa sun hada kansu a jihar Kaduna domin kawo ci gaban zaman lafiya

- Al’umman sun amince su yi aiki tare da jami’an tsaro da kuma samar da bayanai masu amfani

- Kungiyoyin biyu sun hadu da farko lokacin da aka yada jita-jita cewa za’a kai wa al’umman Inyamurai hari

A wannan lokaci da aka rubuta cewa  kasar Najeriya ke cikin tashin hankalin kabilanci, Al’umman Hausawa da Inyamurai a karamar hukumar Jema’a na jihar Kaduna sun yanke shawarar hada kansu domin yaki da masu aikata laifuka a yankin.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa al’umman sun yanke wannan shawarar ne a ranar Litinin, 5 ga watan Satumba, cewa zasu hada kai tare da hukumomin tsaro domin shafe masu laifi.

KU KARANTA KUMA: Shugaban Arewa yayi kira ga zanga-zanga

An yanke shawarar ne a wani gamuwar hadin gwiwa da al’umman biyu sukayi a gurin taron Inyamurai a Kafanchan.

Alhaji Kabir Kasim wanda shine mataimakin babban Limamin Jema’a, shine shugaban taron.

Yace hakkin kowa ne ya goyi bayan hukumomin tsaro ya kuma yi alkawari cewa sauran kabilu za’a hada su a Kafanchan domin a cimma nasara.

Ya bayyana cewa hakan zai taimaka gurin wanzuwar zaman lafiya kamar yadda yake da muhimmaci a kore laifuka a al’umman.

Mr Martin Okoli wanda shine shugaban al’umman Inyamurai a Kafanchan ya shawarci mazauna garin da su bi doka.

Cif Chibuze Akpu wanda shine wakilin al’umman Inyamurai a masarautar Fantswan ya shawarci matasa da su guji aikata abunda zai bata masu sunan su.

KU KARANTA KUMA: Labarai guda 9 da sukayi fice a ranar Juma’a

Anyi wani taro makamancin wannan a tsakanin Inyamura da Hausawa a watan Augusta, bayan jita-jita na cewa ana shirin kai hari ga al’umman Inyamurai dake yankin.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel