Masu Rago sun koka da rashin kasuwa a Kaduna

Masu Rago sun koka da rashin kasuwa a Kaduna

Kasa da mako guda ga bikin Sallah, masu sayar da raguna sun koka da rashin kasuwa wanda ke da alaka da matsin tattalin arzikin da ake fama da shi a kasar

Masu Rago sun koka da rashin kasuwa a Kaduna

Masu sayar da dabbobi a Kaduna sun soma kuka da rashin cinikin dabbobin da ake fama da shi, yayin da Sallah ta ke karatowa, rashin cinikin da aka danganta ga matsin tattalin arzikin da ya sa masu dabbobin da yin kuka da rashin masu zuwa su saya a kasuwar Zango da ke kan titin Bachama, da kuma Rigasa duk a jihar Kaduna, ya kai matuka.

A cewar Kamfani Dillancin Labaran Najeriya, a wadannan kasuwanni da akwai Ragunan da suka yi kwana da kwanaki a wurin, amma babu wanda ya zo ya taya ballatana a sallama masa.

A cewar Kamfanin NAN ya cigaba da cewa, Malam Muhammadu wani mai sayar da raguna a kasuwar sayar da dabbobi da ke kan Titin Bachama, rashin cinikin na damunsu sosai, Muhamamd wanda ya zo daga jihar Sakkwato da Raguna ya ce, ya sayar da raguna 5 ne kacal daga cikin guda 50 da ya zo da su a makon biyun da suka wuce.

Muhammadu ya kuma kara da cewa, “matsin tattalin arzikin da ake fama da shi, ya taimaka matuka ga rashin sayen dabbobin, kuma hakan na shafar aljihunmu, sai dai ba mu fitar da rai ba, kasancewar saura mako guda ga Sallah, muna sa rai mu samu ciniki kafin lokacin, saboda komawa da dabbobin Sakkwato ba karamar hasara ba ce a gare ni.”

Farashin raguna dai sun kama daga Naira 25,00 zuwa Naira 120,00- a cewar mai sayar da dabbobin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel