Cutar Musulmi a Najeriya ta isa haka - MURIC

Cutar Musulmi a Najeriya ta isa haka - MURIC

-Shugaban kungiyar kare hakkin Musulmai a Najeria MURIC ya ce, ana cutar mabiya addinin a Najeriya

-Ya yi kira da ranar Juma’a da ta zama ranar hutu

-Najeriya kasa ce marasa bin addini guda

Cutar Musulmi a Najeriya ta isa haka - MURIC
Farfesa Akintola Ishaq shugaban MURIC, Kungiya mai kare hakkin Musulmai a Najeriya, ya yi ikirarin cewa, ana cutar Musulmai a kasar

Shugaban kungiyar kare hakkin Musulmai a Najeriya Ishaq Akintola, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta daina nuna banbanci tsakanin Kristoci da Musulmai a kasar.

A wata hira da ya yi da jaridar The Punch, Akintola wanda kuma Farfesa ne a fannin koyar da addinin Musulunci ya ce, Najeriya kasa ce da bata bin tafarkin kowanne addini, amma kuma ana cutar da mabiya addinin Musulunci.

KU KARANTA KUMA: A gurfanar da masu wa’azi dake sa kiyayar addini- Soyinka

Shehun malamin ya kuma ce, amma saboda gadon akidun turawan mulkin mallaka da kasar ta yi, Musulmai na shan wahala, ya kuma bayar da misali da inda aka mayar da Lahadi a matsayin ranar hutu ga mabiya addini Krista, yayin da Juma’a kuma take ranar aiki.

Farfesa Akintola ya kara da cewa, duk da cewa kasar babu ruwanta da wani addini, a da, Kristoci a zamanin mulkin mallaka na hutun Krisimeti amma musulmi ba sa hutun Sallar layya da ta Azumi, sai da aka yi gwagwarmaya sannan aka ba Musulmai wannan dama”.

Farfesan ya kuma kara da cewa, “Kristoci sun kakaba mana tsarin hada-hadar kudi da riba wanda ya ke haramtacce ne a Musulunci, amma duk da haka sun ki su bari a kafa bankin Musulunci, sai da Sarki Kano ya yi jan ido tukunna a lokacin da ya ke gwamnan Babban Banki…… Ko a cikin ministocin wannan gwamnati daga  yankin kudu maso gabas da ake da jihohi shida, biyu ne kawai Musulmai, sauran duk Kristoci ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel