Shehu Sani na kira ga Buhari da ya dau mataki ta gaggawa

Shehu Sani na kira ga Buhari da ya dau mataki ta gaggawa

– Sanata Shehu Sani ya soki shugaba buhari a kan rashin zantar da gamayyar matsana tattalin arziki

– Yayi gargadin cewa da yiwuwan yan najeriya su mutu kafin canji ya karaso

– Sanatan ya bayyana cewa guguwar canji ta kwanta

Shehu Sani na kira ga Buhari da ya dau mataki ta gaggawa

Sanata Shehu Sani yayi gargadi ga shugaba Muhammadu buhari akan cewa fa canji da akayi ma jama'a na iya jinkircewa kuma sanadiyar haka yan najeriya su mutu

An zabi Shugaba Buhari ne akan kyakkyawan zaton cewa zai kawo canji amma mutane na ganin yaudararsu yayi saboda a yanzu tattalin arzikin mu ta durkushe.

Jaridar Punch ta bada rahoton cewa sanatan mai wakiltar Kaduna ta tsakiyan yayi kira da shugaba Buhari da ya dau matakai na gaggawa domin shawo kan al'amarin. Sani  ya soki shugaba buhari a kan rashin zantar da gamayyar matsana tattalin arziki Wadanda zasu fidda kasar daga cikin durkushewar tattalin arzikin ta.

KU KARANTA: Melaye yace Buhari ya sallami ministocin tattali da Gwamnan CBN

Yace: “Idan ka kasance kan karagar mulki, kuma kana son kawo sauyin da zai ita shafen mutane, toh dole ne ka sanar da su akan abinda ka keyi. Idan ba haka ba, sai ka kawi sauyin kuma mutanen sun mace.

Sanatan yayi gargadin cewa guguwar jam'iyyar APC fa ta fara kwantawa.

Yace: “Bari in fada muku yadda ta fara, wanda kuma wannan daya ne a kowani shugaba a najeriya. A 1979 da 1999, idan aka samu sabon shugaba, yan najeriya zasu goya masa baya, daga baya suce, muna baka shawara, sai, muna gargadin ka, sai, muna shakkar ka, sai, ba zaka iya ba, sai, bamu sonka. Idan kayi dubi cikin wadannan al'amuran, mutane sun tashi daga soyayya zuwa bashi shawara, kuma wasu na sukanshi,wasu kuma na gargadin shi. Ko shakka babu mutane na gani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel