Danjuma Goje ya bayyana kan siyasa

Danjuma Goje ya bayyana kan siyasa

- Tsohon gwamnan jihar Gombe Danjuma Goje ya ragargaji masu sukar gwamnatin APC

-Ya yi kira ga ‘yan jam’iyyar a jihar Gombe da su zama tsintsiya

-Ya jinjinawa shugabancin jam’iyyar ta kasa da ta dinke barakar jihar

Danjuma Goje ya bayyana kan siyasa
wasu magoya bayan 'yan jam'iyyar  APC  a wani taro

Sanata Danjuma Goje na jihar Gombe ya ce, komai lalacewar gwamnatin APC ta fi ta PDP sau dubu a jihar Gombe.

A cewar jaridar The Nation, tsohon gwamnan jihar Gombe, Danjuma Goje ya furta hakan ne a lokacin da ya ke jawabi a lokacin kaddamar da kwamitin riko na jam’iyyar a jihar wanda manyan jami’an jam’iyyar na kasa suka yi.

KU KARANTA KUMA: Obasanjo yace bai yi magana game da takarar 2019 ba

Sanata Goje wanda kuma shi ne shugaban kwamitin Majalisar dattijai kan kasafin kudi, ya yi kira ga ‘ya ‘yan jam’iyyar a jihar da su zama tsintsiya madaurinki daya a jihar, su kuma kasance tamkar uwa daya, uba daya. Sannan ya kuma ce, rikicin jam’iyyar a jihar ya sa sun rasa wasu abubuwa da yawa daga gwamnatin tarayya.

Tsohon gwamnan ya kuma ci gaba da cewa, a duk lalacewar mulkin jam’iyyar APC a jihar, za ta amfani ‘ya ‘yan jam’iyyar ta hanyar samun mukamai da sauransu, ba kamar yadda gwamnatin PDP a jihar ta ke yiwa ‘yan APC ba.

KU KARANTA KUMA: Sule Lamido ya maganta kan Buhari

Ga manyan jami’an APC na kasa da kuwa Sanatan na cewa, ya yi matukar godiya da suka kawowa ‘yan jam’iyyar dauki a jihar, duk da abubuwan da suka faru a baya, sannan ya kuma yi kira ga ‘yan jam’iyyar da su ba sabbin shugabannin jam’iyyar a jihar hadin kai da goyon baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel