Fani-Kayode ya maganta kan Najeriya da Kenya

Fani-Kayode ya maganta kan Najeriya da Kenya

Femi Fani-Kayode yace wanda Najeriya ta fi kasar Kenya nesa ba kusa ba.

Tsohon Ministan Sufurin Jiragen sama na Najeriya, Femi Fani-Kayode, yace Najeriya fa ba sa’ar Kenya ba je. Ministan ya bada wannan bayani ne ta shafin sa na sada zumuntar zamani na Twitter.

Fani-Kayode ya maganta kan Najeriya da Kenya

Mista Femi Fani-Kayode ya kare Najeriya, yace Kasar Kenya tana bayan Najeriya a kowane fanni.

Femi Fani-Kayode yayi amfani da shafin sa na Twitter mai lambar @realffk, a ranar Lahadin nan inda yace Kasar Kenya ta daina ja da Najeriya. Fani-Kayode yace dole fa kowa ya san matsayin sa, duk lalecewar goma ta fi biyu. Femi Fani-Kayode yace fa duk bacin dan Najeriya to ya fad an Kenya, ko da kuwa Saraki ne.

An dai fara wannan takun-saka ne tsakanin Kasashen biyu bayan da Mark, mai kamfanin Facebook ya kawo ziyara Kasar ta Najeriya, daga nan kuma ya wuce Kenya. Abin dai ya fara ne a Ranar Juma’a nan, bayan da wata ‘yar Najeriya ta saka wani hoton Mista Zuckerberg yana cin abinci, ta kuma ce a Kasar Najeriya abin ya faru. Tuni ‘yan Kasar Kenya suka far mata, har ya kai ta bada hakuri.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya yaba da halin Zuckerberg

Sai dai a wajen irin su Fani-Kayode, abin bai tsaya nan ba, yayi amfani da shafin sa wajen maida martani. Ga wasu daga cikin bayanan nasa:

Maganar gaskiya ita ce, Najeriya ta fi karfin Kenya. Ni na san tarihin Kasar su, ciki da waje. Kenya ba sa’ar Najeriya ba ce.

— Femi Olu-Kayode(FFK) (@realFFK) Satumba 3, 2016

Lokacin da ‘Yan Kasar Kenya suke cin junan su, lokacin mu muna Jami’o’in Oxford da kuma Cambridge

— Femi Olu-Kayode(FFK) (@realFFK) Satumba 3, 2016

Mutanen Kasar Kenya su shafa mana lafiya, dole su san cewa komai lacewar dan Najeriya, ya fi karfin da Kenya, kowane ne shi kuwa.

— Femi Olu-Kayode(FFK) (@realFFK) Satumba 3, 2016

Asali: Legit.ng

Online view pixel