Buhari ya ganawar siri da mai kamfanin Facebooƙ

Buhari ya ganawar siri da mai kamfanin Facebooƙ

A wani labari da dumi-duminsa, shugaba Muhammadu Buhari na wata ganawar sirri da attajiri Mark Zuckerberg mai dandalin sada zumunta na Facebook

Buhari ya ganawar siri da mai kamfanin Facebooƙ
Zuckerberg na gabatarwa da Buhari wani abu daga fasahar zamani a fadar shugaban kasa a Abuja

Jim kadan bayan barinsa kasar zuwa Kenya, Mista Mark Zuckerberg mai dandalin sada zumunta da muhawara na Facebook, ya dawo Najeria, kuma yana ganawa da shugaba Muhammadu Buhari a Abuja.

Buhari ya ganawar siri da mai kamfanin Facebooƙ
Zuckerberg na ganawa da Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbanjo a Abuja

A wata sanarwa da hadimin Shugaba Buhari kan harkokin kafofin yada labarai na zamani, Bashir Ahmed Sharada ya lika a dandalin sada zumunta da muhawara na Twitter, a ranar Juma’a 2 ga watan Sataumba, ya ce, a suna ganawar ne a daidai wannan lokaci.

Buhari ya ganawar siri da mai kamfanin Facebooƙ
Mark tare da wasu yara a inda suke nuna masa irin ta su fasahar a Lagos

Mista Zuckerberg ya kuma gana da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbanjo, daga bisani ya kuma halarci a wani taro a kan kokarin gwamnatin tarayya kan bunkasa ayyukan fasaha a kasar a matsayin babban bako, an kuma shirya wasu kamfanoni guda 30 za su halarci taron, a inda za su gabatar da irin tasu fasahar ta zamani gare shi.

Matashi Mark Zuckerberg wanda ke cikin jerin attajiran da suka fi kowa kudi a duniya, shi ne mai kamfanin Facebook wanda ya kirkira a lokacin yana makaranta, amma kuma ya zama kusan kowa na amfani da shi a duniya wajen sada zumunta da tafka muhawara a intanet.

KU KARANTA: Zuckerberg ya samu karramawa daga manyan yan Najeriya

Attajirin wanda ya ziyarci Lagos a farkon makon nan daga baya ya wuce kasar Kenya, ya bayyana sha’awarsa ga harshen Hausa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel