Sayayyar 'yan wasa a ranar karshe da su ka ba kowa mamaki

Sayayyar 'yan wasa a ranar karshe da su ka ba kowa mamaki

Sayayyar ranar karshe da ya ba kowa mamaki.

Bayan an rufe kasuwar saida ‘yan wasa, NaiJ.com Sports ta duba cinikin da suka fi ba kowa mamaki da aka gudanar a ranar karshe.

Sayayyar 'yan wasa a ranar karshe da su ka ba kowa mamaki

Jack Wilshere ya koma Bornemouth:

Abin ya ba jama’a mamaki da aka ji cewa dan wasa Jack Wilshere zai bar Arsenal, Kungiyoyi kusan 21 suka nemi a saida masu da dan wasan, irin su AS Roma, FC Porto dsr. Kungiyar Bournemouth ce tayi sa’ar daukan aron dan wasan tsakiyar na Kasar Ingila mai fama da raunuka.

Moussa Sissoko a Tottenham:

Dan wasa Sissoko ya taka rawar gani a Gasar Euro 2016 musamman a ranar wasan karhse, ya dauki idanun manyan Kungiyoyi irin su Arsenal, Tottenham da ma Real Madrid. Sai dai Dan wasan ya bayyana cewa yana son ya koma Arsenal, kwatsam sai gas hi an ji ya tafi Kungiyar Tottenham, manyan ‘yan adawan Arsenal din.

KU KARANTA: Joe Hart ya koma Torino

Mario Balotelli ya koma Nice

Abin da kusan ban dariya dai ace dan wasa Mario Balotelli ya koma Kungiyar Nice. Dan wasan da ya bugawa kungiyoyi irin su; Liverpool, Inter Milan, AC Milan da Manchester City tun yana shekara 26 ace ya koma wata Kungiya irin Nice. Wani abin alajabi shine, ba fa aro dan wasan ya tafi ba, ya koma Kungiyar Nice ne din-din-din bayan Liverpool ta katse kwantiragin sa.

David Luiz ya dawo Chelsea FC

Wannan abu ya ba jama’a matukar mamaki, ace David Luiz ya dawo Kungiyar Chelsea? Ko da Kungiyar ta ke neman dan baya, ba Luiz ta ke sa ran saye ba, da abubuwa suka faskara ne ta koma ga tsohon dan wasan na ta. Shekaru biyu da suka wuce Chelsea ta saida dan wasan, sai ga shi kuma ya dawo.

Joe Hart ya tafi Torino

Babu wanda ya taba tunanin cewa Golan Ingila Joe Hart zai bar Man City, ina ma kuma ace ya koma Kungiyar Torino a Kasar Italiya? Ba shakka Torino ta shigo cikin sahun manyan Kungioyi bayan ta dauki aron Babban gola irin Joe Hart.

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel