Sarkin gargajiya ya tsine ma duk wanda yaki zaben Obaseki

Sarkin gargajiya ya tsine ma duk wanda yaki zaben Obaseki

–An gargadi masu zabe a karamar Hukumar Ovia south west a jihar Edo masu niyyan zaben wani koma bayan Godwin Obaseki a zaben da za'a gudanar a ranan 10 ga watan Satumba.

–Sarkin gargajiya ,HRH Patrick Igbinidu ya yi barazanar cewa duk wanda ya zabi wanin Obaseki zai sha la'ana

–Obaseki yace zai ma yan yankin tara mai kyau idan har suka zabe sa a zaben

Sarkin gargajiya ya tsine ma duk wanda yaki zaben Obaseki

Wani sarkin gargajiya , iyasen masarautar Udi , Patrick Igbinidu ya gargadi masu zabe a karamar Hukumar ovia south west a jihar edo masu niyyan zaben wani koma bayan Godwin obaseki a zaben da za'a gudanar a ranan 10 ga watan Satumba.

Sarkin yayi barazanar ne a ranan talata, 30 ga watan agusta yayinda jam'iyyar APC ta je yakin neman zabe Udo, karamar Hukumar ovia south west , yace duk wanda bai zabi obaseki ba na shirin tsinuwa ta bishi.

Yayinda yake bayani akan cigaban kasa, yace , “Mun aike shi ne kuma muna rokon Allah ya bashi nasaran zama gwamna kuma muna da yakinin duk alkawarin da yayu zai cika. Ina farin cikin cewa shine zai cigaba bayan Oshiomole, mun san duk abinda oshiomole ya fara , obaseki zai karasa kuma ya ingantasu. A fada ma lungu da sakon udo cewa obaseki ne zamu zaba a mmatsayin gwamna bayan oshiomole. Kun gani ,wannan shine wanda mutanen udo zasu zaba.

 Dan takaran gwamnan jihar karkashin jam'iyyar APC, Godwin Obaseki ya gode ma sarkin da goyon bayan da yakewa gwamnatin Adams Oshiomole kuma yace za'a mayar da hankali unguwar domin samar da cigaba a wajen. Yace zai yi amfani da arzikin unguwar domin amfanar da mutanen yankin domin su dogara da kansu.

KU KARANTA : Femi Adesina ya gana da Turaki Hassan a fadar shugaban kasa

A bangare guda, cocin Redeemed Christian Church of God (RCCG) Edo Region 13 headquarters (Trinity Sanctuary) da ke Benin City ta zama ofishin kampen Dan takaran gwamnan jihar Edo karkashin jam'iyyar PDP, Mt Ize Iyamu . a rataye hotunan shi a cikin coci gaba daya. Fastocin da ya kamata su dinga ma mutane gargadi sun koma yan siyasa.

 

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel