Shugaba Buhari Ya amince da Kasafin Kudin Birnin Abuja

Shugaba Buhari Ya amince da Kasafin Kudin Birnin Abuja

Shugaba Muhammad Buhari ya rattaba hannu kan kasafin kudin Babban Birnin Tarayya Abuja inda aka tsara kashe Naira Bilyan 241.5 wajen bunkasa birnin a cikin wannan shekarar.

Shugaba Buhari Ya amince da Kasafin Kudin Birnin Abuja

Mai Ba Shugaban Kasa Shawara kan harkokin Majalisa, Sanata Ita Enang ne ya bayyana haka inda ya ce matakin rattaba hannu ya ba hukumar birnin damar aiwatar da manyan ayyukan na ci gaban birnin. Ana dai ci gaba da kokawa kan yadda birnin ya kasance cikin kazanta sakamakon kin kwashe shara a cikin birnin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel