Ina alfahari da harshen hausa- wanda ya kafa Facebook, Zuckerberg (Hotuna)

Ina alfahari da harshen hausa- wanda ya kafa Facebook, Zuckerberg (Hotuna)

-Mark Zuckerberg ya iso kasar Najeriya a ranar Talata, 30 ga watan Augusta

-Wanda ya kafa shafin dasarwan Facebbok ya fadi dalilin da yasa yake kaunar harshen Hausa

-Mutumin wanda ya kasance daga cikin manyan masu kudi goma a duniya ya ziyarci Afrika kashi na farko

Ina alfahari da harshen hausa- wanda ya kafa Facebook, Zuckerberg (Hotuna)

Shugaban Facebook ya bayyana cewa yana alfahari da sanya harshen Hausa a manhajar shafin. Mark Zuckerberg ya fadi hakan ne a ranar farko na ziyarar sa kasar Najeriya, wanda ya fara a jihar Lagas, ziyarar shine ziyarar sa na farko a nahiyar Afrika.

Tuni ya gana da matasan da suke harkar kamfanonin fasahar zamani domin ya kara musu karfin gwiwa.

Wata sanarwa da kamfanin Facebook ya fitar ya bayyana cewa  Zuckerberg ya je Najeriya ne domin harkokin bincike na kasuwanci.

"Mark zai yi saurari jama'a, ya dauki darasi da kuma hikomomi kan yadda Facebook zai taimaka wurin bunkasa harkokin sadarwa a Afirka," in ji sanarwar.

Ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa "zan dauki darasi kan yadda ake kafa kananan kamfanoni a fannin sadarwa a Nijeriya."Wannan wuri ya bani sha'awa sosai, kuma a shirye nake na koyi abubuwa masu da dama".

Ya kuma yi alfahari da amfani da harshen Hausa a manhajar ta Facebook, sannan ya ce za su ci gaba da sanya sauran harsunan Nijeriya.

KU KARANTA KUMA: Labari da dumi-dumi: rikici ya kaure a gidan yarin Kuje, ana barin wuta

Kalli ra'ayoyin 'yan Nijeriya kan ziyarar ta Mista Zuckerberg:

Kididdiga ta nuna cewa mutanen Najeriya sun fi na kowacce kasa masu ma'amala da kafar sada zumunta ta Facebook a nahiyar ta Afirka.

Ya taso ne daga kasar Italiya, inda ya gana da Paparoma Francis, sannan ya yi magana kan muhimmancin samarwa mutane damar yin hulda juna da yanar gizo musamman a wuraren da babu manhajar.

Ina alfahari da harshen hausa- wanda ya kafa Facebook, Zuckerberg (Hotuna)
Mark Zuckerberg
Ina alfahari da harshen hausa- wanda ya kafa Facebook, Zuckerberg (Hotuna)
Mark Zuckerberg with Nigerian youths
Ina alfahari da harshen hausa- wanda ya kafa Facebook, Zuckerberg (Hotuna)

Asali: Legit.ng

Online view pixel