Kungiyar Chelsea Sun Saka Ma Tsohon Dan Wasar Su David Luiz £32m.

Kungiyar Chelsea Sun Saka Ma Tsohon Dan Wasar Su David Luiz £32m.

-Chelsea sun yi tayi mai kyau na dawo da dan wasar su.                                                      

-Chelsea suna kokarin kara karfafa bayan su kafin rufe kasuwar sayen yan wasa.                                                    

-Alessio Ramagnoli da kalidou koulibaly da Chelsea ta taya kungiyoyinsu basu yadda da cinikayyar ba.

Kungiyar Chelsea sun saka ma tsohon dan wasan su mai tsaron baya David Luiz kudi £32 miliyan dan ya dawo kungiyar bayan barin kungiyar da yayi zuwa Paris saint-german.

Kungiyar Chelsea Sun Saka Ma Tsohon Dan Wasar Su David Luiz £32m.
David Luiz

Luiz baya cikin yan wasan da Sabon mai horarwa Unai Emry yake son yayi amfani da su , dan haka Luiz din yake nuna rashin Jin dadin shi na karancin lokacin doka wasar.

Luiz dan shekara 29, dan wasan kasar Brazil, Chelsea ta saida kan kudin da yafi kowane dan wasan baya a duniya miliyan £50 shekara 2 da suka wuce.

Dan shekara 29 ya samu kanshi cikin wadanda akai ta caccaka lokacin da kungiyar Monaco ta doke PSG satin da ya gabata, lokacin da aka canja Luiz din bayan ya janyo ma kungiyar finariti.

Chelsea sun koma zawarcin Luiz bayan kasa biyan kudin dan wasar Napoli na baya Kalidou Koulibaly da kuma kin amincewa da kungiyar Ac Milan da tayi na Miliyan £30 da miliyan £32 ga Alessio Ramagnoli yayin da Chelsea ta taya dan wasan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel