‘Yan wasan Arsenal biyu za su tafi aro

‘Yan wasan Arsenal biyu za su tafi aro

 

– Dan wasan Tsakiya, Jack Wilshere na iya barin Kungiyar.

– Dan bayan nan, Calum Chambers zai tafi Middlesbrough

– ‘Yan wasan na kokarin kara habaka wasan su

‘Yan wasan Arsenal biyu za su tafi aro

‘Yan wasan Kungiyar Arsenal Jack Wilshere da Calum Chambers za su tafi aro

A shekarar 2014 ne Arsenal ta sayi dan wasan bayan nan mai suna Calum Chambers daga Kungiyar Southampton, bayan shekaru biyu kuma sai ga dan wasan zai bar Kungiyar Arsenal din zuwa Kungiyar Middlesbrough.

Dan wasa Calum Chambers zai je aro ne Kungiyar ta Ingila, ganin ko ya babbako da kan sa. Shekaru biyu da suka wuce Arsenal ta sayi dan wasan kan kudi fam miliyan £16m daga Kungiyar Southampton. A wasan farkon sa, kamar da gaske, ya taimaki Arsenal din ta doke Man City da ci 3-0 a Kofin ‘Community Shield’.

Sai dai daga baya dan wasan ya koma benci, bayan da Kocin Arsenal, Arsene Wenger ya zabi ya rika amfani da Per Mertesacker da kuma Laurent Koscielny a baya. An dai take wasanni kusan 17 da dan wasa Calum Chambers a shekarar, amma a shekarar da ta wuce an fara wasanni biyu ne rak da dan wasan. Duk da cewa Arsene Wenger na zuzuta dan wasan, sai dai ya zama dole ya bar Kungiyar domin ganin ya kara habaka wasan sa.

Haka dai kuma da alamun cewa dan wasa Jack Wilshere zai bar Kungiyar ta Arsenal. Dan wasan zai tafi aro wata Kungiyar, da dama dai suna ganin rauni ne ya hana dan wasan yin armashi. Wilshere ya buga wasanni 17 ne kacal gaba daya wancan shekarar, dan wasan na fama da raunuka dabam-dabam.

Manyan Kungiyoyi da dama ke zawarcin dan wasan mai shekaru 24 da haihuwa, sun kuwa hada da Valencia ta Spain da kuma Kungiyar Juventus ta Italiya.

KU KARANTA: DALILIN DA YA SA POGBA YA ZABI KUNGIYAR MAN UTD

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel