Joe Hart da Samir Nasri za su tashi daga Kungiyar Man City

Joe Hart da Samir Nasri za su tashi daga Kungiyar Man City

– Dan wasa Samir Nasri zai koma Kungiyar Sevilla.

– Mai tsaron gida Joe Hart zai koma Torino.

– Sai dai da daman a ganin cewa dan wasan Golan ya ci baya.

Joe Hart da Samir Nasri za su tashi daga Kungiyar Man City

Dan wasa Samir Nasri da Kuma Golan Kungiyar Joe Hart ta Man City za su bar Kungiyar ta Man City

Dan wasa Samir Nasri na daf da komawa Kungiyar Sevilla ta Kasar Spain, dan wasan ya zabi Sevilla ne sama da Besiktas domin kokarin habaka wasan sa, dan wasan dai ya shiga wani hali a Kungiyar ta Man City. Kungiyoyin Sevilla masu rike da Kodin UEFA Cup da kuma Besiktas na Kasar Turkiyya ne suka nemi aron dan wasan.

Duk da cewa dan wasan ya buga wasan da Kungiyar Man City ta kara da West Ham a wannan mako, Dan wasan mai shekaru 29 ya san zai yi wahala a rika taka ta da shi karkashin sabon Kocin Kungiyar, Pep Guardiola. Hakan ta sa dan wasan zai tafi aro Kungiyar Sevilla.

Dan wasa Nasri ya koma Kungiyar Man City ne daga Arsenal a shekarar 2011, bayan Kungiyar Man Utd ta nemi sayen sa, shekaru biyar baya kuma, labarin dan wasan ya canza, sai dai dan wasan na iya tinkaho da Kofunan Premier league har biyu da ya daga a Kungiyar ta Man City.

KU KARANTA: DALILIN DA YA SA POGBA YA ZABI MAN UTD

Haka kuma Golan Kungiyar na Man City Joe Hart, yana Kasar Italiya yanzu haka, dan wasan zai koma Kungiyar Torino aro. Sabon Kocin Kungiyar Pep Guardiola dai ya nuna cewa sam ba zai yi da dan wasa mai tsaron gidan ba. Hart ya buga wasa daya ne kacal karkashin sabon Kocin.

Guardiola ya sayo sabon gola, Claudio Bravo daga Barcelona wancan makon, hakan ya tabbatar da cewa Golan Kungiyar zai zama na uku a jeringiyar masu kamawa Kungiyar. A Kungiyar Torino dai Golan zai samu damar buga wasanni sai dai wasu na ganin dan wasan ya fa ci baya.

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel