A sake duba batun 'Film Village' a Kano -Sarkin Sunusi

A sake duba batun 'Film Village' a Kano -Sarkin Sunusi

-Sarki ya yi kira ga malamai da su rika zurfafa tunani

-Ya kuma bukaci a sake duba batun gina farfajiyar shirya fina-finai a Kano

-Malamai soki shirin gina wurin da cewa zai kawo lalacewar tarbiyya

A sake duba batun 'Film Village' a Kano -Sarkin Sunusi
Sarkin Kano tare da 'yan Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano a lokacin da suka kai masa ziyara a fadarsa

Mai Martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sunusi na II a ya yi kira ga Malamai da kuma Mahukunta da su dinga zurfafa tunani kafin yanke hukunci.

Sarkin na magana ne kan batun gina farfajiyar shirya fina-finai da gwamnatin tarayya ta shirya yi a Kano, amma kuma ta fasa a sakamakon nuna rashin amincewa da malamai suka yi, a bisa dalilin cewa hakan zai dada lalata tarbiyyar matasa.

Sarkin na magana ne a lokacin da ‘yan Hukumar kula da tace fina-finai ta jihar suka kai masa ziyara a karkashin shugabanta Alhaji Isma’il Na Abba Afakallah a fadarsa, a ranar Litinin 29 ga watan Agusta, wanda kuma aka yada kafofin yada labarai na jihar.

Mai Martaba sarki ya kuma ce, “jama’a su daina kallon al’amura da ido daya a dukkan wani abu da ya taso, domin kowanne abu yana da nasa alfanu da kuma nasa aibu…” Sannan ya kuma yi kira da a sake nazari a kan batun, da nufin a tsince abin da ya ke da amfani, a kuma yi watsi da wanda ba zai amfani jama’a ba.

Shirin fim na daya daga cikin hanyoyin da ke samarwa matasa aikin yi da kuma samarwa da gwamantin tarayya kudin shiga idan aka cire harkar mai, malamai sun yi adawa da ginin ne a bisa cewa wurin zai taimaka wajen dada bata tarbiyya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel