Ubangiji zai yiwa Nigeria abubuwa 5 saboda Buhari

Ubangiji zai yiwa Nigeria abubuwa 5 saboda Buhari

Sakamokon kunci da matsin tattalin arziki da ake fama da shi, wani fitaccen mai wa’azin addinin Krista Fasto James Adejoh a Kaduna ya yi ikirarin cewa, Ubangiji ya nuna masa wasu muhimman abubuwa 5 da za su faru da Nigeria a karkashin mulkin Shugaba Buhari, kamar haka;

Ubangiji zai yiwa Nigeria abubuwa 5 saboda Buhari

1 Najeriya za ta farfado: ba kamara yadda kasar ta zoma zama saniyar ware ba a tsakanin kasashen duniya, karsashi da maratabar kasar zai ta dawo.

Ubangiji zai yiwa Nigeria abubuwa 5 saboda Buhari
Kimar Najeriya za ta farfado a idanun Duniya

2 Wani abu da daban zai faru: a cewarsa, ba kamar yadda mutane ke tsammanni ba, akwai wani abu na daban zai faru ga kasar wanda kuma daidai ya ke da canjin da aka yiwa jama’a alkawari.

Ubangiji zai yiwa Nigeria abubuwa 5 saboda Buhari
Jama'ar za su ga bazata a mulkin Buhari

3 Buhari zai ba mutane mamaki: Mai wa’azin Kristan ya ce, Ubangiji zai ba yiwa al’ummar Najeriya bazata ta hanyar shugaba Buhari.

Ubangiji zai yiwa Nigeria abubuwa 5 saboda Buhari

4 Abubuwa za su soma aiki yadda suka kamata: Fasto Adejoh ya ce, Ubangiji zai yi amfani da Shugaba Buhari abubuwa su soma aiki kamar yadda ya kamata, kuma bisa tsarin da aka kaucewa a da.

Ubangiji zai yiwa Nigeria abubuwa 5 saboda Buhari

5 Buhari zai ceto Najeriya: A Fasto James Adejoh wanda ya yi amanna da cewa zaben Buhari a matsayin shugaban Najeriya daga Ubangiji ne, zai fitar da kasar na daga matsalolin da suka addabeta, faston yay a kuma yi hasashen cewa, bayan kyakyawan nazarin halin da kasar ta ke ciki, sauyin da ake nema zai zo nan ba da dadewa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel