Bishiyar ayaba tushe arziki ne a kasar Rwanda

Bishiyar ayaba tushe arziki ne a kasar Rwanda

A kasar Ruwanda, ayaba na daga cikin manyan abincin mutanen. Shin ta yaya suke samun kudi banda ci da suke yi da sayarwa ? wadannan bishiyoyin ayaba na ba su arziki.

Kayan tsabta irin tawul, takardar gusar da kazanta da kuma kunshin jarirai na da karanci a kasar ruwanda. Wasu dalibai 3 daga kasar ingila sunyi bincike akan ayaba kuma suka samo yadda za’a iya amfani dasu wajen kera irin wadannan abubuwan.

Bishiyar ayaba tushe arziki ne a kasar Rwanda

Abu na farko da zaka gani idan ka shiga kasar ruwnda shine bishiyoyin ayaba. Zaka gansu a ko ina. Shin wani amfani mutanen kauyen zasu yi dashi bayan ci.

Wadannan dalibai 2 sunyi bincike akan ayaban kuma suka samo wannan dabara. Sun gano cewa ana iya amfani da bishiyar ayaba wajen hada tawul,takardar gusar da kazanta. Audugar da za’a samu daga jikin bishiyan nada ikon tsotson lema

KU KARANTA : Labari da dumi-dumi: rikici ya kaure a gidan yarin Kuje, ana barin wuta

Matan kasar na amfani da tsimmokara ne lokacin jinin al’adan su,kuma yana janyo musu cututtuka iri-iri ,har mutuwa. Saboda haka, hada auduga daga bawon bishiyar wani salo mai sauki. Kana,ana iya yin shi da wuri. Wannan wata kafa ce da mutanen karkara zasu iya amfani d shi domin kasuwanci da kuma kara koshin lafiyan jama’a.

 

 

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel