Abubuwan da suka faru a Gasar Premier League wannan makon

Abubuwan da suka faru a Gasar Premier League wannan makon

Abubuwan da suka faru a Gasar Premier League makon da ya gabata.

Abubuwan da suka faru a Gasar Premier League wannan makon

Mun dauko maku muhimman abubuwan da suka wakana a zagaye na 3 na Gasar Premier na Ingila. Kungiyoyin Manchester United, Manchester City da Chelsea sun samu nasara a duka wasannin su 3 da suka buga wannan shekarar.

Ga kadan daga cikin manyan abubuwan da suka auku a wannan karo:

Rashford yayi rawar gani:

Dan wasan nan na Man Utd Marcus Rashford, ya zama matashin farko da ya ci wa Kungiyar kwallo karkashin sabon Koci Jose Mourinho. Dan wasan ya ci kwallo a makararren lokaci a wasan da suka buga da Kungiyar Hull City.

Fernandinho ya ci kwallo:

Dan wasan tsakiyar nan na Manchester City watau Fernandinho ya ci kwallon sa Gasar Premier league na farko cikin kusan shekara daya. Rabon da dan wasan ya ga zare, tun wani wasa da Kungiyar City ta buga da West Ham a bara, inda ta ci 3-1.

Ranieri na Leicester ya ciri tuta:

Leicester City ta doke Swansea da ci 2-1 a filin wasa na ‘King Power Stadium’, wannan na nufin Kocin ya samu nasarar sa na 100 kenan a Gasar Premier League. Claudio Ranieri ya zama mutum, bako (ba Baturen Ingila ba) na biyar, da ya taba samun a Tarihi.

Yaushe rabon duniya da ayi yayi; Victor Moses da cin kwallo a Chelsea.

A wasan Chelsea da Burnley, wanda aka tashi 3-0, dan wasa Victor Moses ne yaci ta karshe, wannan de dai kwallon dan wasan na farko cikin shekaru hudu. Moses ya buga wasa aro a Kungiyoyin Liverpool, Stoke City da ma West Ham cikin shekarun da suka wuce.

KU KARANTA: CHELSEA ZA TA HADU DA LEICESTER A WASAN KOFIN INGILA

Jermaine Defoe ya shiga kundin tarihi:

Dan wasan gaban nan na Kungiyar Sunderland, Jermain Defoe, ya shiga cikin jerin ‘yan wasa 10 da suka fi kowa kwallaye a Tarihin Premier League. Ya ci kwallo daya a wasan su da Southampton, inda aka tashi 1-1, yanzu dan wasan na da kwallaye 145 a Gasar EPL.

A mako mai zuwa ne dai za a kara tsakanin Jose Mourinho na Manchester United da kuma kuma makwbata Manchester City da Pep Guardiola.

Asali: Legit.ng

Online view pixel