Chelsea za ta sayi dan wasa daga Inter Milan

Chelsea za ta sayi dan wasa daga Inter Milan

– Kungiyar Chelsea na daf da sayen dan wasa Marcelo Brozovic daga Inter Milan.

– Sai dai har yanzu Kungiyar ta Chelsea na kokarin yarjejeniya da dan wasan.

– Rahotanni sun nuna lallai za a kammala wannan ciniki kafin a rufe tagar saye ko saida ‘yan wasa.

Chelsea za ta sayi dan wasa daga Inter Milan

Chelsea na daf da sayen dan wasan tsakiyar Kungiyar Inter Milan mai suna Marcelo Brozovic Inji Goal.com

Goal.com ta rahoto cewa Inter Milan ta amince da tayin Chelsea na sayen dan wasan ta Marcelo Brozovic, Dan wasa Brozovic asalin dan Kasar Croatia ne, yana kuma buga tsakiya. Amma dai kawo yanzu Kungiyar ta Chelsea ba ta cin ma yarjejeniya ba da dan wasan.

Rahotanni sun nuna cewa akwai ganin yiwuwar kammala wannan ciniki kafin Ranar 31 ga wata da za a rufe kasuwar cinikin ‘yan wasa, yanzu dai haka, ana ta tattaunawa tsakanin Kungiyoyin. Dan wasan dai yana neman karin albashi idan har zai koma Landan da taka leda.

KU KARANTA: CHELSEA ZA TA KARA DA LEICESTER

Kungiyar ta Chelsea kuma ba za tayi kakara da wani dan wasan ta ba wajen wannan ciniki, kamar yadda aka yi ta yada cewa dan wasa Cesc Fabregas zai bar Kungiyar. Cesc Fabregas din dai bai buga wasan Chelsea da Burnley ba, inda Chelsea ta samu nasara da ci 3-0. Dan wasan ya kuma bayyana cewa babu wani rikici tsakanin sa da Sabon Kocin Kungiyar, Antonio Conte. Yanzu haka ma dai, Kasar Spain ba ta gayyaci Fabregas ba zuwa wasannin da za ta buga da Kasar Belgium da kuma Liechtenstein.

Kungiyoyi da dama, musamman a Ingila suke neman dan wasa Brozovic, dan wasan dai ya koma Kungiyar Inter Milan din ne daga Dinamo Zagreb a Watan Junairun 2015. Dan wasan tsakiyar ya kuma ci kwallaye 8 cikin wasanni 51. Chelsea dai ta sayi N’Golo Kante da Michy Batshuayi wannan shekarar.

KU KARANTA: BARCELONA TAYI SABON GOLA

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel