Wurare guda 6 da ake neman mai a Najeriya

Wurare guda 6 da ake neman mai a Najeriya

Shugaban hukumar tace albarkatun man fetur na kasa NNPC Maikanti Baru ya zayyano wasu wurare guda shidda inda a yanzu haka gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari take kokarin neman man fetur.

Maikanti yayi wannan jawabin ne yayin da yake tarbar shugabancin kungiyar masu hako main a kasa a karkashin jagorancin shugabanta Nosa Omorodion a Abuja a ranar alhamis 25 ga watan agusta.

Wurare guda 6 da ake neman mai a Najeriya

Maikanti ya basu shawaran da su dage wajen cin moriyar tarin arzikin man fetur da iskar gas dake jibge a wasu yankunan kasar nan guda shida. Ya kara da cewa gwamnatin kasar a shirye take don ganin tayi kyautata ma masu niyyar zuba jari a harkar. Wurare guda shida ya ambata sun hada da:

1. Yankin Chad

Anambra

Bida

Dahomey

Gongola/Yola

Benue Trough

Maikanti ya kara baiwa kungiyar shawara dasu dage wajen ganin sun samu cimma yarjejeniyar hadin gwiwa tsakanin su da hukumomi don cin gajiyar man fetur da iskan gas dake yankin.

Shiko jagoran tawagar, Omorodion ya taya shugaban hukumar NNPC murnan nada shi da aka yi, inda yace kungiyar NAPE zata karrama shi a watan nuwambar bana sakamakon rawar da yake takawa sashin harkar hako ma’adan mai.

Tun biyo bayan umarnin da shugaban kasa ya bayar na fara hako man fetur ne dai hukumar ta soma kokarin hakar man a yakin arewa maso gabas na kasar nan sati biyu da suka wuce.

Asali: Legit.ng

Online view pixel