Ana zargin Goodluck Jonathan da hannu cikin magudin zabe

Ana zargin Goodluck Jonathan da hannu cikin magudin zabe

Jaridun Litinin 29 ga Agusta suna maida hankali ne kan manyan labarai irin su shedar da Chief Olu Falae  ya bayar wadda ke alakanta Goodluck Jonathan  da N100m ta magudin zabe, barazanar da shugaba Buhari ke ma tsageru da kuma niyyarsa ta musayar 'yan matan Chibok da 'yan Boko Haram dake tsare

Ana zargin Goodluck Jonathan da hannu cikin magudin zabe

Chief Olu Falae ya zargo tsohon shugaba Goodluck Jonathan da hannu cikin N100m na zabe da jam'iyyar PDP ta bashi

The Punch ta ruwaito tsohon sakataren gwamnatin tarayyar na cewa cikin wata wasikar email da ya rubuta ma tsohon shugaban kwamitin amitattu na PDP Chief Tony Anenih, wadda ke alakanta Jonathan da N100m ta kudin zabe

A cikin wasikar email din Anenih, ya ce yana isar da umurnin tsohon shugaba Jonathan ne . "A cikin wasikar email din, Anenih ya gaya ma Chief  Falae wanda shine shugaban jam'iyyar SDP cewa shugaba Jonathan ya amince a bada N100m matsayin yarjejeniya dake akwai tsakanin PDP da SDP gabannin zaben shugaban kasa" wata majiya daga EFCC ta gaya ma the Punch. "Ya kuma bukaci Falae ya bada asusun bankin da za'a saka kudin"

Jaridar Vanguard na magana ne kan barazanar da shugaba Muhammadu Buhari ke ma tsagerun Neja Delta na yi masu yadda yayi ma Boko Haram idan basu daina fasa bututun mai ba a yankin. Shugaba Buhari ya ambaci haka ga masu daukar labarai yayin da yake halartar taron kasa da kasa na Tokyo kan ci gaban Afrika karo na shidda koko sixth Tokyo International Conference on African Development (TICAD) a Nairobi, Kenya. Amma shugaban na cewa, gwamnatinsa na shirye ta tattauna da tsagerun kan abubuwan da ke damun yankin

Jaridar The Nation ta ruwaito mai ba shugaba Buhari shawara kan sadarwa da fadakarwa, Mallam Garba Shehu, na ambatar cewa shugaban na alakanta maganganu da ake yi game da 'yan matan Chibok da siyasa

"Abinda muke cewa shine gwamnati mai ci shirye take ta tattauna da shugabannin Boko Haram na gaskiya. Kuma idan basu son magana da mu Kai tsaye, suna iya zabo kowace hukumar kasa da kasa mai zaman kanta wadda aka san da zamanta, su kuma tabbatar masu suna rike da yaran, kuma suna son Najeriya ta saki wasu daga cikin shuwagabanninsu wadanda ya kamata su sun sansu. Idan suka yi haka, kuma ta hannun sabbin shugabannin Boko Haram, to shirye Najeriya take ta tattauna kan sakinsu"

The Sun ta ruwaito shugaba Buhari na cewa gwamnati ba zata bata lokaci da kudi ba kan "hanyoyi marasa tabbas" wadanda ke ikrarin sanin inda yaran suke. "Muna son sakin yaran cikin koshin lafiya domin mika su cikin sauri ga iyayensu" ya ci gaba da cewa.

Jaridar Guardian ta jiya 28 ga Agusta na cewa kididdiga na nuna cewa kudin shiga da gwamnati ta samu cikin watanni shidda na wannan shekarar na N1,159.05 billion Wanda kashi 51.3 ne ya kasance kasa da kashi 8.6 na kasafin kudi na kwatankwacin tsawon lokacin da ya wuce

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel