Laifukan Jonathan da Tampolo a yankin Niger Delta

Laifukan Jonathan da Tampolo a yankin Niger Delta

Mista Johnny Micheal shi ne shugaban gidauniyar cigaban mazauna Egbema/Gramatu da ke Okerenko, a masarautar Gbaramatu a jihar Delta, a hirarsa da Legit.ng ya bayyana laifukan Goodluck Jonathan da kuma Tampolo ga alummar yankin

Laifukan Jonathan da Tampolo a yankin Niger Delta
Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan

Yaya ka ke kallon rikicin yankin Niger Delta?

A gidan gwamnatin jihar Bayelsa tsagerun yankin suka sha alwashin wanzar da tashin hankali idan Jonathan bai ci zabe ba, an yi wannan a gaban gwamnan Bayelsa Seriake Dicson, da Kingsley Kuku, da Asari Dokubo da kuma Tampolo, don haka Kungiyar da ka ke ji ta tsagerun Niger Delta Avengers ba wasu ba ne illa Tampolo da yaransa.

Ko yaya ka ke ganin tuhumar da gwamnati ta ke yiwa Tampolo?

Tampolo na ikirarin cewa ba shi da kudi, a ina ya samu wadannan biliyoyin nairori da ya jibge a banki EFCC ta kulle? Kuma saboda shi mutane da yawa ke rasa rayukansu, ana kuma lalata mana muhalli, tattalin arziklin Najeriya kuma na dada lalacewa, a duk  kudaden da Tampolo ya ke da shi, bai taba cire kwandala ya kafa wata gidauniyar taimakawa Okerenko ba, mutanenmu na fama da fatara da yunwa amma ba za su iya magana ba, saboda ana tsoronsa, ni kuma ba na tsoronsa,

Jonathan da ya azurta Tampolo, ya kasa gina hanya a mahaifarsa Otouke, ba kuma ya jin harshensa na  Ijaw, da ya na ji, da ya saurari abin da al’ummar yankin dangane da bakar wahala da azabar da suke ciki.

 Ko da me kabilar Ijaw ta amfana daga mulkin Jonathan na shekaru 6?

Mun amfana da rarrabuwar kai, ya kuma kawo mana fatara, baya ga rasa rayukan al’umma. Saboda ya nada mutanen da ba su dace ba a manyan mukamai daga nan, mutanen da sa tare da jama’arsu, daga su sai ‘ya ‘yansu. Yanzu EFCC ta sa su a gaba, tana kwace kadarorinsu da kudaden da suka sata. Ma ga inda za su sa kansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel