Dan fashi ya mutu a hadarin mota

Dan fashi ya mutu a hadarin mota

–Wani dan fashi ya bakunci lahira yayinda yake kokarin arcewa

–Wata motace  ta bige shi yayinda a wata unguwa a Jihar Legas

–Sauran yan fashin sun shiga hannu

Wani dan fashin da ke gudu kan titi ya bakunci lahira ne a karshen wannan makon da ya gabata ya mutu ne yayinda yake kokarin arcewa daga jami’an yan sanda da ke biye da shi a unguwan Ijanikin a Jihar Legas.

Dan fashi ya mutu a hadarin mota

An bada rahoton cewa dan fashin yam utu a take a lokacin. Daya daga cikin abokan fashin shi, Bassey Eyo ,22, ya shiga hannun yan sanda ofishin Ijanikin da ke Jihar Legas.

Rahotanni sun bayyana cewan hadarin motan ya faru ne misalign karfe 9:30 na dare a tashan Ojo da ke babban titin Lagos-Badagry.

An tattara cewan jami’an yan sanda sun kama yan fashin wadanda ke tare hanya suna kwace dukiyoyin jama’a. kakakin kwamishanan yan sandan Jihar Legas, Dolapo Badmos, ta bayyana cewa an kai gawan dan fashin dakin ajiy gawawwaki.

KU KARANTA : Sojoji sun kama masu garkuwa da mutane

Yan sanda sun samu sa’an kama barayi yayinda mazauna Oghara da ke karamar hukumar Ethiope West a Jihar Delta suke ta murnan mutuwan wani gagararren dan fashi mai suna Ono Okeribo, a unguwan.

 

 

 

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel