Abun tausayi karnukan makwabta sun cinye wani mai shekaru 83

Abun tausayi karnukan makwabta sun cinye wani mai shekaru 83

A Jacksonville, Florida, karnukan makwabta sun cinye wani tsoho mai shekaru 83, Micheal Downing a raye.

Abun tausayi karnukan makwabta sun cinye wani mai shekaru 83

Makwabtan sa Mackenzie Partin da Eddie Edwaeds sun tsinci gawan Downing kusa da gurin zuba shara a ranar Juma’a 19 ga watan Augusta, da misalign karfe 4 na rana.  Da yake Magana da gidan talbijin din WFTV9, Partin ya bayyana cewa karnukan sun shigo ta wani rami dake katangan da ya raba gidan Downing daga gidan mai Karen, karnukan suka kuma janye wanda abun ya faru dashi zuwa yankin su.

 “wannan ne mugun abu da na taba gani a tsawon rayuwana. Kaso talatin cikin dari kawai ne abubuwan da suka rage a jikinsa. Sunja shi zuwa guinsa, sun kuma hadu sun cinye shi.”

An bayyana karnukan guda hudu a matsayin Rottweiler da kuma Jamus. An ruwaito cewa karnukan sun cire kafafuwan wanda abun ya faru a kansa sun kuma cinye naman jikin sa da kuma kansa lokacin da suka kai masa harin.

KU KARANTA KUMA: Binciki Obasanjo, shi ya gabatar da cin hanci da rashawa- Waku ga Buhari

An rahoto cewa gurin kiwon Jacksonville Animal Care and Protective Services suna shirin bayyana karnukan a matsayin hatsari wanda zai janyo a kashe su.

A nan gida Najeriya munji cewa wani mutumi Joachim Chinakwe Iroko, ya sanya wa karen sa suna Buhari, wato sunan shugaban kasa wanda hakan ya haifar da cece kuce a tsakanin mutane da dama, har ya kai ga tsare mutumin mai shekaru 40 a duniya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel