Kungiyar Barcelona tayi sabon gola

Kungiyar Barcelona tayi sabon gola

 

– Barcelona ta saye sabon Gola.

– Kungiyar ta maye gurbin Claudio Bravo da ya koma Kungiyar Man City.

– An sayo sabon dan wasan Jasper Cillessen ne daga Ajax Amsterdam.

Kungiyar Barcelona tayi sabon gola

Kungiyar Barcelona ta saye sabon Gola mai suna Jasper Cillessen daga Kungiyar Ajax Amsterdam domin maye gurbin Claudio Bravo wanda ya koma Kungiyar Man City ta Ingila.

Barcelona ta saye dan wasan nan mai tsaron raga Jasper Cillessen mai shekaru 27 daga Kungiyar Ajax Amsterdam na Kasar Nederland. Dan wasan ya sanya hannu kan yarjeniyar shekara biyar da Kungiyar.

An saye dan wasa Jasper Cillessen ne kan kudi kusan fam miliyan 13 (Na farashin Dalar EURO), farashin dai nayi iya tashi da fam miliyan 2 nan gaba. Barcelona ta sanya kudin saida dan wasan a kan fam miliyan 60 (Na farashin EURO).

KU KARANTA: GOLAN BARCELONA , CLAUDIO BRAVO YA TASHI

Dan wasan ya iso Kulob din ne a ranar Alhamis da safe, bayan an yi masa gwaji, ya sanya hannu bisa kwantiragin na sa ba tare da bainar jama’a sun sani ba. Golan dai zai zama mataimakin Golan farko na Kungiyar watau Marc Ter Stegen. Sabon Dan wasan zai maye gurbin tsohon dan wasan Kungiyar, Claudio Bravo wanda ya koma Kungiyar Manchester City ta Ingila da kama wasa.

Cillessen ya kamawa Kasar sa ta Nederland wasanni har 30, ya fara bugawa Kasar ta sa ne dai a shekarar 2013, tun bayan nan kuwa, ya zama shi ne mai tsaron ragar, a Gasar World Cup 2014, Kasar Nederland din ce ta zo ta uku, Cillessen kuma ke tsare da ragar.

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel