Leicester City za ta kara da Chelsea a Kofin Ingila

Leicester City za ta kara da Chelsea a Kofin Ingila

– Zakarun Premier League, Leicester City za su fafata da Chelsea a Kofin Ingila

– Kungiyar Manchester City ne suka lashe wannan kofi shekarar da ta gabata.

– Kungiyar Stoke za ta buga da Hull City, inda kuma Kungiyar Man Utd za taje Northampton Town.

Leicester City za ta kara da Chelsea a Kofin Ingila

Anyi duron Gasar Kofin ‘English Football League Cup’ na zagaye na uku. A wannan zagaye Leicester City za ta fafata da Chelsea.

A duron da aka yi, Kungiyar Arsenal ta Arsene Wenger za ta je gidan Nottingham Forest, Chelsea kuma za ta je gidan Leicester City. Yayin da Swansea City kuma za ta karbi bakuncin Zakarun Gasar Manchester City a gida. Man City ce ta lashe gasar wancan karo, bayan ta doke Liverpool a bugun finariti.

KU KARANTA: VICTOR MOSES YACI KWALLO A GASAR KOFIN INGILA

Leeds united za ta kara da Kungiyar Blackburn Rovers, Kungiyar QPR Watau Queen Park Rangers za ta je Gidan Sunderland a zagayen nan uku. Haka kuma Kungiyar Accrington Stanley za ta karbi bakuncin West Ham United.

A Gasar cin wannan kofi Kungiyar Fulham za ta je gidan Bristol City, inda kuma Bournemouth da Preston North End za su kara. Tottenham za ta buga da Gillingham a Gidan ta. Kungiyar Everton ma za ta karbi Norwich. Derby County za ta buga da Kungiyar Liverpool, Liverpool ta kai wasan karshe a wannan kofi shekarar da ta gabata.

Kungiyar Man Utd ta Jose Mourinho za ta buga da Northampton town, Reading kuma za ta hadu da B & H Albion. Newcastle kuma za ta buga tsakanin ta da Wolves, sai kuma Stoke City da Hull City.

pic.twitter.com/kWteEBVN9x

— EFL Cup (@EFLCup) August 24, 2016

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel