Daure mutumin da yayi wa Shugaban Kasa takwarar kare: Babu ruwan Buhari

Daure mutumin da yayi wa Shugaban Kasa takwarar kare: Babu ruwan Buhari

– Mai magana da yawun-bakin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Garba Shehu yace babu hannun Shugaban Kasa game da daure Joachim Chinakwe

– Garba Shehu yace masu alakanta daure mutumin da Buhari, ba su ma san waye Shugaban Kasar ba.

– An daure Joachim Chinakwe bayan ya nadawa karen sa suna Buhari.

Daure mutumin da yayi wa Shugaban Kasa takwarar kare: Babu ruwan Buhari

Fadar Shugaban Kasa tayi magana dangane da mutumin nan da aka kama, aka daure domin ya sanya wa karen sa suna Buhari, tace sam, babu ruwan Shugaban Kasa da wannan aiki.

Mataimakin Shugaban Kasar kan harkar sadarwa, Garba Shehu, ya bayynana cewa masu tunanin akwai hannun Shugaban kasa wajen daure mutumin nan da ya sanyawa dan sa suna Buhari, sun jahilci wanenen Muhammadu Buhari, Shugaban Kasa. Garba Shehu yayi wannan bayani ne a kafafen watsa labarai na zamani.

KU KARANTA: WOLE SOYINKA YA FADA WA BUHARI CEWA...

Garba Shehu yace bari yayi amfani da wannan dama yayi bayani ga jama’a, duk masu yunkurin jefa Shugaban Kasa cikin wannan maganar ba su san me suke fada ba. Garba Shehu ya bayyana cewa, Shugaban Kasar na da sha’awar irin zanen da ake yi a jarida domin ba’a, kuma ko yaushe ya gan su, suna ba sa dariya kwarai, har ya sanar da mutane.

Garba Shehu yace shirme ne har wani yayi tunanin cewa Shugaban Kasar zai ba ‘yan sanda umarnin kama wanda ya yi masa takwarar kare. “Idan Buhari ya dauki jarida, abin da yake fara dubawa ciki shine irin wadannan zane…ba mamaki sai dai ya gani kurum yayi dariya” Garba Shehu y aba jama’a shawara da su karanta duk abin da yake faruwa ga mutumin da aka dauren, maimakon tsoma hannun Shugaban Kasa cikin wannan abu.

An dai kama Mista Joachim Fortemose Chinakwe a ranar Talatan nan saboda ya rada wa karen sa suna Buhari, bayan da wani Bahaushen makwabcin kasuwanci sa ya kai sa kara cewa ya nadawa karen sa sunan mahaifin sa, Alhaji Buhari. Tuni dai an bada belin mutumin, bayan yayi kwana uku a daure.

Asali: Legit.ng

Online view pixel