Manchester City sun sayi mai tsaron ragar Barcelona.

Manchester City sun sayi mai tsaron ragar Barcelona.

_ Claudio Bravo ya koma kungiyar Manchester City.

_ Dan kasar Chile ya sanyama kungiyar ta Man City hannu na tsawon shekaru hudu.

_ Ana tunanin dai Joe Hart zai koma wata kungiyar.

Manchester City sun sanar da siyan sabon dan wasan su, wato mai tsaron ragar Barcelona Claudio Bravo na tsawon shekaru hudu. Bravo dai yana da basira sosai, wanda ya kawoma Barca cigaba daya basu daman daukar kofin Laliga a jere har sau biyu, kuma ya taimakama kasarshi Chile suka samu nasaran lashe gasar Copa America.

Manchester City sun sayi mai tsaron ragar Barcelona.

Dan shekara 33, ya lashe kyaututuka a kasarsa har guda 106, sannan kuma shine Kaftin din kasar. Haka kuma yaci kyauta a gasar Copa America da aka buga na 100 a kasar Chile, inda Chile ta doke Argentina a wasan karshe inda wasan yakai matakin bugun dagakai sai maitsaron raga, wanda wannan shine karo na farko da kasar Chile ta taba samun nasara.

Yaje Barcelona a shekarar 2014 daga Real Soceidad sannan kuma yaci kofuna har kala 8 acikin shekara biyu da zuwansa kungiyar ta Barcelona, Yayi wasa 75 kuma yana daga cikin jerin yan wasan Laliga da sukafi kowa hazaka na shekarar 2014/2015. Haka kuma an zabeshi a matsayin mai tsaron ragar dayafi kowane mai tsaron raga hazaka a gasar Copa American shekaran 2015 da 2016, dakuma samun daman buga wasa a kungiyar kowane lokaci.

Yadai sanya hannu ne a sakamakon yabashi da Pep Guadiola yayi alokacin da yake son mai tsaron ragar daya dace dashi. Haka kuma zuwan dan kasar Chilen zaisa Joe Hart yabar kungiyar inda Everton da Liverpool suka nuna suna zawarcin dan wasan.

 

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel