Niger Delta Avengers sunyi barazanar fallasa sojoji

Niger Delta Avengers sunyi barazanar fallasa sojoji

-Tsagerun Niger Delta Avengers sun karyata kashe Sojoji a Nembe, jihar Bayelsa

-Yan bindigan sun zargi Sojoji dayi harkan mai a yankin ba kan doka ba

-Sunyi barazanar sakin hotuna da bidiyo na abunda sojoji suka aikata

Kungiyar tsagerun Niger Delta sunyi barazanar sakin hotuna da kuma bidiyon yadda sojojin Najeriya da aka mayar yankin Nager Delta domin su samar da zaman lafiya, sun shi harkan mai ba bisa doka ba.

Barazanar ya biyo bayan rahotannin tsaro da ya danganta yan bindigan da kashe sojoji a Nnembe, jihar Bayelsa.

A wata sanarwa daga yan bindigan a ranar Laraba, 24 ga watan Augusta, dauke da sa hannun Brigadiya janar Mudoch Agbibibo, kungiyar na zargin cewa wanda aka kama kan zargin kashe sojoji ba ainayin mabiya bayan Timipre Silva bane kuma yayi da’awar cewa an basu magamai daga tsohon gwamna kafin zaben jihar Bayelsa.

KU KARANTA KUMA: Hawa'u Sale na neman taimako cikin gaggawa

Kungiyar Avengers tayi da’awar tana da faifan kasetin  yawancin rundunar sojoji a yankin Niger Delta na yanda suke tafiyar da harkan man da ba bisa doka ba.

A halin yanzu, kungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB) a ranar Laraba 24 ga watan Augusta, sun karyata rahotannin wasu yankin cewa kun rabu kashi-kashi a kungiyar , cewa kungiyar na hade kuma suna ci gaba da neman Biafra.

Shugaban watsa labarai na kungiyar IPOB, Emma Powerful, yace kungiyar karkashin shugabancin Mazi Nnamdi Kanu, bata canza ba kuma yan kungiya na biyayya babu tantama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel