Arsenal na zawarcin James da Morata, Madrid kuma Sanchez

Arsenal na zawarcin James da Morata, Madrid kuma Sanchez

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta fuskanci kakkausan suka daboda gazawarta a kasuwar cinikayyar yan wasa.

A bana dai yan wasa uku kacal Arsenal ta siya duk da cewa yan wasanta da dama sun samu rauni iri iri, yan wasan sune Granit Xhaka, Takuma Asano sai kuma Rob Holding. Amma a yanzu kocin Arsenal, Arsene Wenger ya nuna sha’awar sa a kan yan wasa biyu na kungiyar Real Madrid.

Arsenal na zawarcin James da Morata, Madrid kuma Sanchez
Sanchez

Dama dai a baya Wenger ya bayyana cewa akwai wasu cinikayya biyu da yake jira su nuna. Don Balon ya dauko rahoton cewa Wenger na sha’awar siyan James Rodriguez da Alvaro Morata, yayin da su kuma Real Madrid ke zawarcin Alexis Sanchez.

A cewar majiyar tamu, Arsenal na neman ayi canji tsakanin dan wasan gaban Sifen Morata da dan wasan Chile Sanchez, inda ita kuma talabijin Chilevision ta ruwaito cewa Arsenal na neman James.

Rahotannin jita jita na nuna cewa Wenger yayi kasa a gwiwa wajen siyan Lacazette, Draxler, Vardy, Higuain, Mustafi da Mahrez.

Asali: Legit.ng

Online view pixel