Dan wasa Victor Moses ya ci kwallo a Chelsea

Dan wasa Victor Moses ya ci kwallo a Chelsea

 

– Dan wasan Najeriya Victor Moses ya ci kwallon sa ta farko karkashin Koci Antonio Conte.

– Rabon Moses da cin kwallo a Chelsea tun shekarar 2012 kafin ya koma Liverpool.

– Hakanan dan wasan Najeriya nan Ighalo ya ci wa Watford.

Dan wasa Victor Moses ya ci kwallo a Chelsea

Ba sa ban-ba: Dan wasa Victor Moses ya ci kwallo a Chelsea, rabon da hakan ta faru, yau fiye da shekaru uku kenan. Haka kuma dan wasa Ighalo na Watford ya jefa kwallo duk a jiya.

Dan wasan Super Eagles dinnan Victor Moses ya jefa kwallon san a farko cikin kusan shekaru hudu, kuma wannan ne kwallon na farko da dan wasan ya ci karkashin Sabon Koci Antonio Conte. Chelsea dai ta samu doke Kungiyar Bristol Rovers da ci 3-2 a wasan cin kofin gida Ranar Talatan nan.

Rabon da ace Moses yaci kwallo tun wani wasa da suka ci 3-1 da suka buga da Kungiyar Basel a shekarar 2012, a shekarar 2013 ne kuma dan wasan ya koma Liverpool aro. A jiya dai Moses ya jefa kwallon ne bayan Sabon dan wasa Michy Batshuayi ya ci ta farko a mitni na 30. Batshuayi ya kata ta biyu a minti na 49. Sai dai Kungiyar Bristol Rovers sun rama duka ta ‘yan wasa Peter Hartley da Ellis Harrison.

READ ALSO: YAN WASAN NAJERIYA SUN DAWO GIDA

Da dan wasan yake magana a shafin Kungiyar bayan an kammala wasan, sai yace: “Idan kuka duba Kungiyar yanzu haka, za ku ga duk kowa na nan, kuma cikin lafiya, hakan zai taimaka sosai. Za muyi kokarin mu cigaba da cin wasannin mu, sai dai wannan kuwa ba abu ne mai sauki ba kodan. Kamar yadda kuka sani, irin wadannan Kungioyi sun fi wahala karawa…”

Haka Dan wasan gaban Najeriya, Odion Ighalo ya jefa kwallo a wasan da aka ci su, dan wasan ya ci kwallo guda daya, sai dai Kungiyar Gillingham ta kora su daga Gasar EFL din bayan an kara lokaci da ci 2-1.

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel