Jawabin Jaridu : Kerry ya ba Buhari shawarar yadda za'a murkushe Boko Haram

Jawabin Jaridu : Kerry ya ba Buhari shawarar yadda za'a murkushe Boko Haram

Kanun labarun jaridun yau ranar Talata 24 ga Agusta sun ta'allaka ne kan ziyarar kwana biyu da sakataren harkokin waje na Amurka John Kerry ya kawo ma Najeriya da kuma sauran abubuwan chikin gida

Jawabin Jaridu : Kerry ya ba Buhari shawarar yadda za'a murkushe Boko Haram

The Sun, ta ruwaito Kerry na mai cewa yayi amanna amfani da karfi kadai ba zai kawo karshen matsalolin tsaro ba. Ya ci gaba da cewa yana bukatar gwamnatin tarayya da ta binciki dalilan da yasa Boko Haram ke kaima 'yan Najeriya hare hare. Kerry yace:

"Boko Haram na tunkaho cewa bata da wata manufa baya ga kona makarantu da wuraren ibada tare da kashe mutane da jikkata su abinda ya saba ma addini". Amma duk da wannan ta'addancin, Kerry ya ba gwamnati da hukumar soja shawara da su sami amincewar jama'a, ya kara da cewa ba za'a iya shawo kan tsageranci da muzgunawa ko tsoratawa ba. Kerry, ya kuma yaba ma shugaba Muhammadu Buhari kan yaki da cin hanci da rashawa da kuma kokarinsa na kwato kudaden da aka sace. Ya ci gaba da cewa cin hanci da rashawa a duniya ya kai yawan $2.6 trillion, kudin da sun Isa su ba jama'a rayuwa ingantatta

The Guardian ita ma ta ruwaito Kerry na baiwa gwamnatin tarayya shawara yadda za'a shawo kan ta'addanci. Sakataren na magana ne yayin da hukumar sojan kasa ke ikrarin jima shugaban Boko Haram Shekau mummunan rauni tare da kashe manyan kwamandojin kungiyar a wani hari na musamman da aka kai. Kerry na yaba ma Najeriya da kwato yankuna daga Boko Haram tare da kubutad da dubban mutanen da ta Kama cikin shekara guda da ta wuce. Yana mai kiran haka "ci yaba mai muhimmanci".

Jawabin Jaridu : Kerry ya ba Buhari shawarar yadda za'a murkushe Boko Haram

Ita kuma jaridar The Punch na magana ne game da kiran taron gaggawa da kungiyar kiristocin Najeriya shiyyar arewacin kasar yayi game da kisan mutane takwas a Talata-Mafara cikin jihar Zamfara da kuma kisan wani pasto na cocin Redeemed Christian Church of God, Luka Ubangari, a Unguwan Anjo, jihar Kaduna da ake zargin Fulani makiyaya da aikatawa. Rohoton na cewa za'a yi taron a Maiduguri ranar 26 ga Agusta inda za'a tattauna abubuwan tare da gazawar gwamnati wajen kama masu aikata laifuffukan. An dai kashe mutane takwas ranar Litinin 22 ga Agusta yayin da wani gungun masu zanga-zanga suka kona gidan wani wanda yayi kokarin kubutar da wani dalibi da ake zargi da yin sabo. A ranar ne kuma wasu mutane da ake zargin Fulani makiyaya ne suka kashe wasu mutane ukku har da Ubangari a Unguwan Anjo na karamar hukumar Jema'a cikin jihar Kaduna.

Rohotannin Vanguard kan kasuwanci na cewa, ranar Laraba 24 ga Agusta babban bankin kasa (CBN) ya dakatar da bankuna tara daga saye da sayar da kudaden waje har sai sun maido da kudaden kamfanin mai na kasa (NNPC) zuwa asusun kasar guda daya da ake Kira Treasury Single Account (TSA). Ana zargin bankunan tara da boye $2.12 billion mallakin (NNPC) da kin maida kudin zuwa TSA kamar yadda gwamnatin tarayya ta umurci ayi. Wannan a cewar masharhanta ya saba ma umurnin da aka bada wanda ya fidda NNPC daga tsarin TSA.

The Nation ta bayyana bankunan tare da kudaden da ke wajensu kamar haka. United Bank for Africa (UBA) $530m; First Bank of Nigeria (FBN) $469m; Diamond Bank Plc ($287m); Sterling Bank Plc ($269m); Sky Bank Plc ($221m); Fidelity Bank ($209m); Keystone Bank ($139); First City Monument Bank (FCMB) $125m;da Heritage Bank ($85m).

 

 

 

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel